Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Zamfara, ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda gwanin takarar Gwamnan Jihar na jami’yyar PDP.
Wannan dai na zuwa ne yayin da kotun ta yi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar tun a watan Mayu wanda Alhaji Dauda Lawal ya zama zakara.
- ISWAP da Boko Haram sun kashe mayakansu 30
- PDP ta mayar da Wike dan kallo a kwamitin yakin neman zaben Atiku
Bayanai sun bayyana cewa, daya daga cikin manema takarar kuma tsohon dan Majalisar Tarayya, Alhaji Ibrahim Shehu ne ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotun.
Da yake yanke hukuncin a wannan Juma’ar, Mai Shari’a Aminu Baffa Aliyu, ya ce korafe-korafen da mai karar ya shigar a cikin takaradun bayanai mai shafi 109 na da madogara da hujjoji.
Mai Shari’a Aminu ya ce gudanar da sabon zabe ne zai tabbatar da adalci a tsakanin duk bangarorin da shari’ar ta shafa.
Sai dai wani lauyan gwamnati da ke wakiltar PDP a jihar, Barista Bashir Abubakar Masama, ya ce za su yi nazari a kan hukuncin da kotun ta yanke gabanin daukar matakin da ya dace.
Barista Masama ya ce za su daukaka kara.