A ranar Talata wata Kotun Majistire da ke Kano ta yanke wa wasu maza biyu, Muhammad Sani mai shekaru 24 da Saddam Ali mai shekaru 24 hukuncin bulala 12 ga kowannensu bayan samunsu da tabar wiri da wasu kayan maye.
Matansa biyu wadanda ba a bayar da adireshinsu ba, sun gurfana a gaban kotun da laifin mallakar tabar wiwi da wasu ababe masu gusar da hankali.
Alkalin da ya jagoranci zaman Kotun, Mista Farouk Ibrahim, ya yankewa ababen zargin biyu hukuncin ne bayan sun amsa laifinsu na mallakar miyagun kwayoyi.
Alkali Ibrahim ya umarci da a yi wa kowane daya daga cikin matasan biyu bulala 12 bayan sun roki kotun da ta yi musu sassauci.
Jami’in dan sanda wanda ya gabatar da kara, Mista Muhammad Bichi, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne da misalin karfe 9.00 na safiya a ranar 21 ga watan Dasimba a Unguwar Plaza da ke Karamar Hukumar Fagge a Kano.
Bichi ya ce, wasu jami’an ’yan sanda da ke sintiri a sashen Fagge sun cafke wadanda ake tuhuma dauke da kwalaye 10 na kwayar ‘Rafanol’ da kuma curi guda na tabar wiwi da wata kwalba daya dauke da wani ruwa da aka tabbatar na maye ne.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito, jami’in dan sandan ya ce wannan laifi da matasan biyu suka aikata ya saba wa sashe na 403 cikin dokokin Jihar Kano.