Wata kotun majistare a Jihar Ogun, ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 19 da ake zargi da satar kayayyaki da suka kai Naira miliyan hudu.
Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta E.O Adaraloye ya bayyana wa kotun cewa ana zargin matashin ne da aikata laifin fashi da shiga gida ba baisa kai’ida ba.
- Kotu ta daure ’yan majalisa saboda dukan abokiyar aikinsu
- ’Yan Najeriya sun koka da karancin sababbin takardun kudi a bankuna
Dan sandan ya kuma ce wanda ake zargin ya haura gidan wani mutum mai suna Bolarinde Jonathan, inda ya saci akwatin talabijin da karafunan Janareta na Naira miliyan hudu.
Ya ce jami’an tsaron sa kai ne suka kamo matashin, sannan suka mika shi ga ’yan sanda.
Insfektan ya ce laifin dai ya saba wa sashi na 411 (1)(2), da na 412 na kundin manyan laifukan jihar na 2006.
Matashin dai ya musanta zargin, kuma Alkalin kotun Misis A.O Adeyemi ta bayar da shi beli kan N100,000, da masu tsaya masa da suka mallaki kwatankwacin kudin belin.
Adeyemi ta kuma ta dage karar zuwa ranar 26 ga watan Janairu domin ci gaba da sauraron shari’ar