✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ayyana Minista a matsayin Sanatan Filato bayan soke zabe

Kotun dai ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ne

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta soke zaben Sanatan Filato ta Kudu a Jihar Filato, Napoleon Bali, sannan ta ayyana Ministan Kwadago, Simon Lalong a matsayin sabon sanata.

Kotun dai ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, bayan ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ta soke nasarar Bali na jam’iyyar PDP.

Lalong dai ya tsaya takarar ce a karkashin jam’iyyar APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, amma bayan an ayyana cewa ya sha kaye a zaben, Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya nada shi Minista.

A cewar kotun, jam’iyyar ta PDP ta saba umarnin kotu kan kin shirya manyan taruka a matakan Mazabu, Kananan Hukumomi da Jiha tun a shekara ta 2021.

A sakamakon haka ne kotun ta ce bai halasta PDP ta tsayar da ’yan takara ba a zabukan Jihar.

Kotun dai wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a E.O Williams-Daeoud, ta ce kotun baya ta yi daidai da ta ayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben saboda dukkan tarukan da PDP ta yi a Jihar ba halastattu ba ne.