✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta aike da mijin da ake zargi da karya hannuwan matarsa mai juna biyu kurkuku

Zai ci gaba da zama a tsare har zuwa 15 ga watan Agusta

Kotun Majistare da ke zamanta a Fada a Zariyan Jihar Kaduna ta tisa keyar wani miji zuwa gidan gyaran hali bisan zarginsa da karya hannuwan matarsa sannan ya ji mata raunuka.

Kotun, a ranar Laraba, ta ce mutumin mai suna Abdulkudus Yusuf, zai ci gaba da zama a kurkuku har zuwa ranar 15 ga watan Agustan 2023 bisa tuhumar da ake masa na raunata matar tasa mai suna Sa’adatu Habibu.

Tun farko dan sanda mai gabatar da kara Sarki Abdullahi, ya shaida wa kotun cewa, “A ranar 29 ga Yuli, 2023, wani mai suna Abdullahi Habibu ya kai kara ofishin ’yan sanda da ke Fada, bisa zargin yunkurin halaka ’yar uwarsa wadda mijinta mai suna Abdulkudus Yusuf ya yi ta hanyar karairaya mata hannuwa da huda mata jiki da kwalba da kuma yunkurin yanke mata nono, wadda ya sabawa sashi na 243 da 223 na kundin dokokin Jihar Kaduna.”

Da kotu ta tambayi wadda ake tuhumar ko ya aikata abin da ake tuhumarsa sai ya musanta kuma ta sake tambayarsa ko yana da lalurar hauka nan ma ya ce a’a.

Mai Shari’a Ibrahim Sa’idu Baban Ja’eh ya tura shi zaman kaso har sai ranar 15 ga watan Agusta 2023, domin ci gaba da sauraron karar.

A halin da ake ciki, yanzu haka matar mai suna Sa’adatu Habibu na kwance a asibitin Wusasa a Zariya, inda take jinyar raunukar da ta samu.