✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ’yan canji 17 a gidan yari a Kano

Kotu ta yanke wa ’yan canji 17 a Kasuwar WAPA da ke Kano hukuncin daurin wata shida a gidan yari.

Kotu ta yanke wa ’yan canji 17 a Kasuwar WAPA da ke Kano hukuncin daurin wata shida a gidan yarin.

Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa na Babbar Kotun Jihar Kano ya yanke musu hukunci ne bayan samun su da laifin aiki babu lasisi.

Sai dai kotun ta ba su zabin biyan tarar Naira dubu 50 bayan sun amsa laifin da aka gurfanar da su a kai.

Aminiya ta ruwaito a makon jiya cewa ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kai samame a Kasuwar WAPA, inda suka kama wasu ’yan canji 17 kan zargin laifin aiki babu rajista.

A lokacin samamen jami’an tsaron sun kama kudaden kasashen waje da suka hada da Sefa 68,000 da kuma Rupee 30,000 a hannunsu.