✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tashi kunnen doki a wasan ’yan sanda da tubabbun ’yan daba a Kano

An gudanar da wasan ne don kyautata alaka tsakanin bangarorin biyu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta buga wasan sada zumunta tsakaninta da tubabbun ’yan daba a jihar.

A ranar Laraba ne bangarorin biyu suka barje gumi a wasan kwallon kafa da aka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano.

An buga wasan ne da misalin karfe 2 na rana, inda aka tashi kowa na da ci daya.

Rundunar ’yan sandan ta ce ta shirya wasan ne a matsayin wani mataki na samar da yanayi mai kyau tsakaninta da tubabbun ’yan daban.

A baya, rundunar ta fitar da jerin sunayen wasu ’yan daba da suka yi kaurin suna, inda ta bayyana tana neman su ruwa a jallo.

Hakan dai na zuwa ne bayan mutuwar wani jami’in dan sanda a unguwar Yakasai da ke jihar sakamakon fadan daba da ya kacame tsakanin wasu kungiyoyin daba biyu da ba sa ga maciji da juna.