✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Nijar ta bude iyakarta da makwabta 5, ban da Najeriya

Sai dai ba a bude ta Najeriya da Benin ba

Mako daya bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, gwamnatin sojin kasar ta sanar da bude iyakokinta da makwabtan kasashe biyar, amma ban da Najeriya.

Kakakin gwamnatin kasar ne ya sanar da hakan yayin wani jawabi a gidan talabijin din kasar ranar Laraba.

Ya ce an bude iyakokin ne na kasa da kuma na sama ga kasashen Mali, Burkina Faso, Algeria, Libya da kuma Chadi.

Gwamnatin ta kuma nada sabbin Gwamnoni ga Jihohin kasar guda takwas.

Sai dai gwamnatin ta ce ya zuwa yanzu iyakokinta da Najeriya da kuma Jamhuriyar Benin, za su ci gaba da zama a rufe.

Har yanzu dai ana ci gaba da zaman dar-dar a kasar yayin da wa’adin da Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta bayar na a dawo da hambararriyar gwamnati ko ta mamaye kasar, yake dada karatowa.

A cewar ECOWAS, dole ne a dawo da Mohammed Bazoum kujerar tasa, ko ta fuskanci fushin dakarun kungiyar. Sai dai gwamnatin sojin ta gargadi ECOWAS da kada ta kuskura ta tura dakarun nata idan tana son zaman lafiya.