Babbar kotun Abuja da ke zamanta a Gwagwalada ta kama wata mai ’ya’ya biyar da laifin damfarar jama’a ta hanyar amfani da sa hannu irin na tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Marigayi Malam Abba Kyari.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ce ta gurfanar da wacce ake zargin a watan Yunin 2022.
An tuhumi matar ne da laifuka biyar da suka shafi zamba cikin aminci da damfara da kuma sanya hannu na bogi.
Laifukan sun saba wa sashe na 13 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka da sashe na 320 (b), 366 na dokokin Penal Code sakin layi na 89 na Arewacin Najeriya.
- An kama dan shekaru 75 da miyagun kwayoyi
- NAJERIYA A YAU: Gwamnatin Zamfara Ta Sa Zare Da Ta Tarayya Kan Yaƙi Da ’Yan Bindiga
Shaidun da aka gabatar sun nuna cewa wadda ake tuhumar ta yi damfara ne da wata takarda ta ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da kuma sa hannunsa.
Masu gabatar da kara sun gabatar da wata wasika inda aka ce Abba Kyari na umurtar shugaban ICPC ya dauki mutane uku aiki a hukumar kai-tsaye.
Sai dai kuma, Marigayi Abba Kyari, a wata rubutacciyar wasika da aka gabatar a gaban kotu a matsayin shaida, ya ce shi da ofishinsa ba su ba da izinin rubuta wasikar da matar ta sanya wa hannu.
Mai shari’a Ibrahim Mohammad ya ba da umarnin tsare ta gidan yari sannnan dage ranar yanke hukunci zuwa ranar 16 ga watan Mayu.