✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan shekaru 75 da miyagun kwayoyi

Jami'an NDLEA sun kama miyagun kwayoyi guda miliyan 3.4 da kuma kwalaben Kodin guda 344,000 a lokaci guda a Legas

Wasu tsofaffi masu ’shekaru sama da 7o sun shiga hannun hukuma kan dillanin miyagun kwayoyi a jihohin Binuwai da Ekiti.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sun cika hannu da wani tsoho mai shekaru 75 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 7.5 a kauyen Oke-Asa da ke Karamar Hukumar Ijero-Ekiti LGA of Ekiti State.

Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi, ya sanar cewa jami’an Hukumar sun kuma kama wani tsohon mai shekaru 70 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 15.6 a garin Makurdi na Jihar Binuwai a ranar Alhamis.

Sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta ce jami’anta sun kama miyagun kwayoyi guda miliyan 3.4 da kuma kwalaben maganin tari na Kodin guda 344,000 a garin Abule Ado da ke Karamar Hukumar Amuwo Odofin a Jihar Legas, kuma wasu mutane uku da ke alaka da kwayoyoin sun shiga hannu.

A cewar Babafemi, an fara kama wasu kwantainoni biyu da wata tirela cike da kwayoyin, kafin daga bisani jami’an hukumar su kai samame babbar ma’ajiyar, inda suka kama ragowar miliyiyoyin kwayoyin a ranar Alhamis 9 ga Mayu, 2024.

“Dirbobin biyu daga cikin motocin masu shekaru shekaru 25 da kuma 30 sun shiga hannu tare da wani dan shekara 51, amma diraben mota ta ukun ya tsere,” in ji sanarar hukumar.