Alkalin-Alkalan jihar Akwa Ibom, Mai Shari’a Ekaette Obot, ya aike da wani lauya mai fafutukar kare hakkin bil-Adama, Inibehe Effiong, kurkuku na tsawon wata daya.
Lauyan ne dai ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook da sanyin safiyar Laraba.
- An damke magidanci ya yi wa agolarsa ciki a Ekiti
- Dan siyasa ya yi karar bokansa a EFCC bayan faduwa zaben neman takara
Ya ce, “Alkalin-Alkalan jihar Akwa Ibom, Mai shari’a Ekaette Obot, ya aike da ni gidan yarin Uyo na tsawon wata guda, saboda kare Leo Ekpenyong, a shari’ar zargin bata suna tsakaninsa da Gwamnan Udom Emmanuel.”
Daga bisani kuma ya wallafa bayanan abubuwan da suka wakana da suka kai ga aike wa da shi gidan yarin a shafinsa na Twitter.
Ye ce, “Alkalin ya umarci wakilin jaridar Premium Times da ya fice daga kotun. Sai na ce masa tun da shari’ar a bude a ke yin ta, bai kamata a hana jama’a kallonta ba. Hakan ce ta sa alkalin ya yi umarnin na ci gaba da sharhina.
“Yanzu dai an aike da ni gidan yarin Uyo. Babu abin da na yi. Ko damar kare kaina ba a ba ni ba, kafin a yanke hukuncin. Akwai lauyoyi biyu da ke cikin kotun da suka nemi gafarar alkalin, amma ya yi kemem cewa dole ya daure ni.
Hukuncin dai na zuwa ne bayan ya kare wanda ake tuhuma, Leo Ekpenyong, a karar da Gwamna Udom ya maka shi a kotun.
A shari’ar dai mai lamba HU/279/2019, tsakanin Gwamnan da Leo Ekpenyong, alkalin ya yanke hukunci bayan an same wanda ake zargi da laifi, inda ya umarce shi ya biya Gwamnan Naira miliyan daya da rabi.
Sai dai daga bisani lauya Effiong ya shigar da sabuwar kara yana neman a jingine wancan hukuncin saboda ya ce ba a ba wanda yake karewa ba cikakkiyar damar kare kanshi. Daga bisani dai kotun ta amince da bukatar lauyan.