✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami mafi girma tun 2017

Wannan gwajin makami mai linzami shi ne cikon na bakwai da Koriya ta Arewa ta yi a bana.

Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami wanda shi ne mafi girma tun bayan wanda ta harba a shekara ta 2017.

Makamin da Koriya ta Arewa ta harba a ranar Lahadi, shi ne mafi girma da karfi da ta yi gwajinsa tun bayan zaman Joe Biden shugaban Amurka.

Bayanai sun ce an harba makamin mai linzami daga Jagang inda Koriya ta Arewan ta saba harbawa da ke gabar tekun gabashin kasar.

Makamin mai linzami ya yi gudun kilomita 800 a cikin mitoci 30 daga wurin da aka harbashi a tafiyar kololuwa ta kilomita dubu biyu kafin ya fada a cikin tekun Japan.

A cikin wata sanarwa da ya bayyana, Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya ce Koriya ta Arewa na nesa da yin amana a kan bukatar kasashen duniya na yin watsi da gwaje-gwajen makaman nukiliya, lamarin da ya sanya ya kira taron gaggawa na Tsaron Kasarsa.

Wannan gwaji wanda shi ne na bakwai tun farkon wannan shekara na zuwa ne a daidai lokacin da China kawarta ke shirin karbar bakwancin wasannin Olympic na sanyin hunturu, yayin da Koriya ta Kudu za ta gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Maris da ke tafe.