Wata kotu a Koriya ta Kudu, ta saki tsohon shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol, bayan da ta yi watsi da kama shi, duk da cewa ana ci gaba da bincike kan zargin da ake masa.
Yoon, wanda aka dakatar daga mulki, an tsare shi ne tun a watan Janairu bayan da ake zarginsa da ƙoƙarin kifar da mulkin farar hula.
A ranar 3 ga watan Disamban 2024, jami’an tsaro sun kai masa samame bisa zargin tayar da zaune tsaye.
Bayan an sake shi, Yoon ya fito daga gidan yari yana murmushi, sannan ya sunkuyar da kai domin nuna godiya ga magoya bayansa da suka zo ganinsa.
A ranar Juma’a, kotu ta soke umarnin da aka bayar na kama shi, inda ta ce babu isassun hujjoji da ke tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi.
Duk da haka, ana ci gaba da shari’a kan batun tsige shi daga mulki.
Masu gabatar da ƙara sun ce za su mayar da hankali kan gabatar da hujjoji a gaban kotu maimakon ɗaukaka ƙara kan sakinsa.
Idan har kotun tsarin mulki ta tabbatar da tsige shi, Koriya ta Kudu dole ne ta gudanar da sabon zaɓen shugaban ƙasa cikin kwanaki 60.
Duk da haka, ana sa ran za a ci gaba da shari’ar Yoon, ko da kuwa an sauke shi daga mulki gaba ɗaya.