✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar daji ta kashe mutum 24 a Koriya ta Kudu

Gobarar ita ce mafi muni cikin gomman shekaru, sannan ta tilasta wa sama da mutane 27,000 tserewa daga muhallansu.

Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa.

Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu maso gabashin kasar.

Har ila yau, ta kuma tilasta wa kusan mutum 27,000 ƙaurar gaggawa bayan ta datse tituna da kuma na’urorin sadarwa kamar yadda mazauna yankunan da ke neman tsira da rayukansu suka sanar.

Wani jami’in Ma’aikatar Kare Mutane ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum 18 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wutar dajin baya ga waɗanda suka jikkata.

Sai dai daga bisani kafofin watsa labarai ciki har da BBC da CNN sun ruwaito cewa adadin waɗanda suka rasu ya kai 24 a dalilin gobarar.

A wani batun da ya shafi ƙoƙarin kashe wutar kuma wani jirgin sojin Koriya ta Kudun mai saukar ungulu ya faɗi da safiyar nan inda matuƙinsa ya rasu a ƙoƙarin dakile gobarar mai haddasa barna.

Alƙaluman da muhukunta suka fitar sun nuna cewa kimanin mutum 26 ne suka jikkata a dalilin gobarar dajin wadda ta ɗaiɗaita wani wurin bauta mai tsohon tarihi na mabiya addinin Buddha da ake kira Gounsa da ke yankin Uiseong.

Wani mutum tsaye yana kallon yadda gobarar dajin ta ɗaiɗaita wani wurin bauta mai tsohon tarihi na mabiya addinin Buddha da ake kira Gounsa da ke yankin Uiseong.