Majalisar Dokokin ƙasar Koriya ta Kudu ta tsige Shugaba Yoon Suk-yeol saboda dokar sojin da ya sanya na wucin gadi, wadda ta haifar da bore a ƙasar.
Shugaban ƙasar wanda ke rabin wa’adin mulkin ya rasa kujerarsa ne bayan magoya bayan tsige shi sun yi rinjaye a Majalisar.
Karo na biyu cikin kwanaki takwas je nan da ’yan majalisar dokokin ƙasar suka kaɗa ƙuri’ar neman tsige Shugaba Yoon Suk-yeol.
Mutum 204 daga cikin ’yan majalisar dokokin sun kada ƙuri’ar goyon bayan tsige shi a yayin da wasu 85 ba su amince ba, uku kuma suka ki jefa kuri’a, sannan an soke kuri’u takwas.
Al’ummar kasar sun fara bukukuwa bayan fitar sanarwar rinjayen tsige Shugaban, bayan kammala kada ƙuri’ar da aka yi a sirrance a zauren majalisar mai mambobi 300.
Duk da haka masu adawa da shugaban na ganin ba su gama cin ma gurinsu ba tukuna.
Shi ma shugaban kasar ya bayyana cewa zai garzaya kotu domin ƙalubalanci tsigewar da aka yi masa.