Masu amfani da wayar salula a koyausshe sun samu mafita a ƙasar Koriya ta Kudu bayan da mahukunta suka samar musu da fitilun taimaka musu yayin zirga-zirga don kare su daga auka wa haɗari.
Wani marubuci Trung Phan ya yaɗa wani bidiyo a kafar sada zumunta ta X, da ke nuna sabon tsarin a shingen wucewar ababen hawa.
An wallafa bidiyon ne tare da taken: “Koriya ta Kudu ta sanya fitulun alamar da za ta bai wa masu tafiya suna kallon wayoyinsu alamar wucewa ko tsayawa.”
Masanin masana’antu Shrinivas Dempo ma ya yaɗa wannan bidiyo a shafinsa na X (Twitter), inda ya kira masu wayar hannu kamar wasu gumaka da hankalinsu ke kan wayar koyaushe.
Ya rubuta, “Alamar zamani: Alamomin zirga-zirga sun gangara zuwa matakin titi a mashigar Seoul ta yadda mutanen da suke manne wa wayar salula za su iya ƙetare hanyoyin cikin sauƙi ba fargaba yayin amfani da wayoyinsu.
Gwamnatin Koriya ta Kudu ta aiwatar da tsarin alamar faɗakarwa da ke aika saƙo ga wayoyi idan masu tafiya sun taka titin zirga-zirgar ababen hawa.
Sakamakon ƙaruwar yawan haɗɗura a kan titi, an fara sanya fitulun zirga-zirga a kan titi a wani ɓangare na gwaji aikin tun a shekarar 2019.
An yi haka ne don sanar da masu tafiya a ƙasa, saboda tsaron lafiyarsu wajen tsallaka hanya yayin da suke kallon wayarsu da kuma kula da kansu lokacin da suke tafiya a ƙasa a lokaci guda maimakon su kalli sandunan da suke ɗauke da alamomin dokokin hanya. (indiatimes)