✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani

Matakin daga babbar ƙawar Iran ɗin zai kawo ƙarshen irin takurar da ƙasashen Yamma ke yi wa Tehran

Akwai yiwuwar ƙasar Koriya ta Arewa mai ƙarfin makaman nukiliya za ta taimaka wajen gyara tashoshin nukiliyan Iran da hare-haren Amurka suka lalata da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya a Iran.

Wani masani mai suna Ankit Panda daga cibiyar zaman lafiya ta kasa da kasa ta da ke Amurka, ne ya bayyana hakan, baya Amurka ta kai hare-hare kan tashoshin nukiliya na ƙasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Ankit Panda, yana bayyana cewa matakin zai kawo ƙarshen irin takura da ƙasashen Yamma ke yi wa Iran.

Hakan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai a matsayin keta hurumin ’yanci da kuma tsaron ƙasar Iran.

Hakan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai a matsayin keta hurumin ’yanci da kuma tsaron ƙasar Iran.

Ta bayyana cewa, “Amurka da Isra’ila su ne kanwa uwar gani a rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, sakamakon yake-yake da ƙoƙarin Isra’ila na faɗaɗa girman ƙasarta, tare sa smaun goyon bayan ƙasashen Yamma.

“Ya kamata al’ummomin duniya masu goyon bayan adalci su fito da murya ɗaya aula’anci wannan abin da Amurka da Isra’ila ke yi, kuma su taka musu burki,” in ji sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa (KCNA) ya ruwaito.

Ƙawancen soji tsakanin Iran da Koriya ta Arewa ta jima, kuma ana zargin ta taimaka musu wajen haɗawa da musayar makamai masu linzami masu gudun walƙilya masu cin dogon zango.

Ankit ya ce ba lallai ne Koriya ta Arewa ta taimaka wa Iran wurin ginawa ko hanzarta ƙera makaman nukiliya ba, domin gudun kada makaman su je Amurka. Idan hakan ya faru, Amurka na iya gano lagon fasahar makaman Koriya ta Arewar.

Amma dai akwai yiwuwar Koriya ta Arewar za ta iya, lura da yadda ke da ƙwarewa wajen fasahar makamai da kuma yadda a baya da yawaita taimako ta wannan bangare ga Rasha, wata babbar ƙawar Iran.