✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami awa 5 bayan Kamala Harris ta bar yankin

Gwajin na zuwa ne awa 5 bayan Kamala Harris ta kammala ziyara

Koriya ta Arewa ta harba wasu makamai masu linzami masu gajeren zango a teku, awa biyar bayan Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris ta kammala ziyara a Koriya ta Kudu.

Yayin ziyarar dai, Kamala ta jaddada aniyar kasarta ta tabbatar da taimaka wa kawayenta na nahiyar Asiya ta fuskar tsaro.

Wannan dai shi ne karo na uku da kasar ke yin gwajin makamin a cikin mako daya kacal, a kokarin da take yi na fadada makamanta da kuma nuna wa Amurka cewa karanta ya kai tsaiko a bangaren makamai masu linzami.

Koriyar dai ta harba makaman ne a yankin Sunchon da ke Kudancin Pyongan wajen misalin karfe 11:48 da 11:57 a agogon GMT.

Rundunar Sojin Japan ita ma ta ce ta shaida harba makaman.

Koriya ta Arewa dai ta harba makaman masu gajeren zango ne ranar Laraba, lokacin Kamala Harris na Japan, sannan ta sake jefa wani kafin barin Kamalan zuwa Washington ranar Lahadi.

Mataimakiyar Shugaban ta Amurka dai ta kammala ziyarar tata ta kwanaki hudu a nahiyar Asiya da tattaunawar da ta yi da Shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk-yeol, sannan ta je kan iyakar Koriyoyin biyu, inda ta yi jawabi kan barazanar da Seoul ke fuskanta daga Pyonyang.

Amurka dai na da dakarun sojan ruwa akalla 28,500 da ta grike a Koriya ta Kudu domin taimaka mata daga barazanar Koriya ta Arewa, kuma a cikin makon nan za su gudanar da wani atisayen gwajin karfe na musamman.