Za a iya cewa kurinkus ta faru ta kare game da jita-jitar da aka yi ta yadawa a kan ficewar Madugun Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga Jam’iyyar PDP tare da komawa Jam’iyyar NNPP da ake ganin Kwankwaso ya farfado da ita.
’Ya’yan Jam’iyyar PDP sun rika tururuwar barin jam’iyyar suna komawa NNPP, inda a ranar Lahadin da ta gabata dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa NNPP inda ya ce rashin adalcin jam’iyyar ce ya janyo ficewarsa.
Sai dai kasa da awa 48 da ficewar Abba Gida-Gidan daga PDP sai Madugun Kwankwasiyyar da kansa, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayar da sanarwar ficewarsa daga PDP a cikin wata takardar da ya mika ga mazabarsa.
Alhaji Shehu Wada Sagagi shi ne Shugaban Rikon Kwarya na Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ya bayyana rashin jin dadi kan ficewar Madugun Kwankwasiyyar inda ya bayyana hakan a matsayin nakasu ga Jam’iyyar PDP.
“A gaskiya ba mu ji dadin jin wannan labari ba, domin rashi a jam’iyya komai kankantarsa koma-baya ne ga jam’iyya ballantana kuma manyan ’yan siyasa kamar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Abba Gida-Gida.
“Ficewasu nakasu ne ga jam’iyya,” inji shi.
Ya ce, “Mun yi iyakar kokarinmu don ganin sun ci gaba da zama a wannan jam’iyya amma ba mu samu nasara ba.
“Muna fata daga yanzu ba za mu sake samun irin haka ba.”
Wadansu na ganin shigar Sanata Rabi’u Kwankwaso da Injiniya Abba Kabir Jam’iyyar NNPP za ta ba jam’iyyar karfin da ake ganin za ta zama barazana ga Jam’iyyar APC.
Sai dai Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Ahmad S. Aruwa ya ce, Jam’iyyar APC ba ta girgiza da jin wannan labari ba.
“Ana ta surutu wai Abba da Kwankwaso sun shiga Jam’iyyar NNPP, wannan ba barazana ba ce gare mu domin bikin magaji ba ya hana na magajiya,” inji shi.
Farfesa Kamilu Sani Fagge Masanin Kimiyyar Siyasa ne a Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana sauyin shekar da ’yan siyasa ke yi a matsayin rashin akida ta siyasa wanda kuma yake kawo wa siyasar kasar nan tarnaki.
“Wannan yana nuna cewa a yanzu an bar siyasar akida, siyasa ta zama ta kasuwar bukata. Duk wanda bai samu biyan bukatarsa a jam’iyyar da yake ba, sai ya tattara kayansa ya koma wata.
“Wannan ya sa siyasar kasar nan ba ta ci gaba,” inji shi.
Sai dai akwai sauran rina a kaba a Jam’iyyar PDP lura da cewa jagororin jam’iyyar masu biyayya ne ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Tuni Kwamitin Gudanarwar Jam’yyar PDP na Kasa (NWC), ya ba da sanarwar rushe shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano da ke goyon bayan Sanata Kwankwaso.
Matakin na zuwa ne bayan umarnin da wata Babbar Kotu da ke Abuja ta bayar na hana jam’iyyar rushe shugabancin da ke karkashin jagorancin Shehu Wada Sagagi.
A sanarwar da ta fitar ta hannun Sakataren Tsare-Tsaren Jam’iyyar ta Kasa, Alhaji Umar M. Bature, PDP ta ce sun yi la’akari da Sashi na 29(2)(b) da sashi na 31(2)(e) da suka bai wa jam’iyyar damar rushe shugabancinta.
Sannan jam’iyyar ta ce ta kafa kwamitin rikon kwarya a jihar karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Atta da sakatarensa Barista Baba Lawan.
Jam’iyyar PDP ta rushe shugabancin ne bayan ficewar Sanata Kwankwaso daga jam’iyyar a ranar Litinin, inda ta zargi wadansu magoya bayansa da neman yi mata sakiyar da ba ruwa.