✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofuna hudu Manchester City za ta lashe a bana -Kocin City Pellegrini

Kocin kulob din Manchester City da ke Ingila Manuel Pellegrini ya hori ’yan kwallonsa da su zage damtse na ganin sun lashe kofuna hudu a…

Kocin kulob din Manchester City da ke Ingila Manuel Pellegrini ya hori ’yan kwallonsa da su zage damtse na ganin sun lashe kofuna hudu a kakar wasa ta bana. Kofunan sun hada da na gasar Premier da ke Ingila da na Carling da ake wa lakabi da Capital One Cup da kuma na kalubale (FA) da kuma kofin zakarun kulob-kulob na Turai watau Champions League.
Ya yi wannan kalami ne jim kadan bayan da kulob din ya lallasa na West Ham United a gasar cin kofin Carling a matakin kusa da na karshe (Semi-Fainal) wasa zagaye na biyu da ci 3-0.&nbsp  West Ham da ci 9-0.<br />Yanzu dai kulob din City ya kai matakin wasan karshe kenan inda ake sa ran zai fafata a tsakanin kulob din Sunderland ko na Manchester United&nbsp