Kocin Chelsea, Thomas Tuchel, ya ce karawa da Manchester City a karkashin jagorancin Pep Guardiola a wasan kusa da na karshe, wato semi final, na Gasar Cin Kofin FA abin farin ciki ne, amma ba zai yi dadi ba.
A wata hira da ya yi da BBC a kan karawar da kungiyoyoin biyu za su yi, Tuchel ya ce Guardiola na da wani imani mai karfi da yake cusa wa ’yan wasanshi a zuciya.
- Real Madrid Da City Sun Fito ‘Semi-Final’ A Gasar Kofin Zakarun Turai
- Chelsea Da PSG Sun Yanki Tikitin Zagayen Daf Da Na Karshe A Gasar Kofin Zakarun Turai
“[Hakan yakan sa] Su yi amanna da abin da suke yi, don haka yana da matukar wahala a bata musu wasa, yana da matukar wahala a karya musu kwarin gwiwa, yana da matukar wahala a dandana musu kudarsu”, inji Tuchel.
Da karfe 5:30 na yammacin ranar Asabar ne dai kungiyoyin za su kece raini a Wembley.
Tuchel ya kara da cewa akwai tazara a tsakanin Man City da Chelsea, amma kungiyarsa za ta yi dukkan mai yiwuwa don ganin ta rufe ta.
Wannan karawa da Chelsea dai na cikin kalubalen da Man City ke fuskanta a burinta na lashe duk wata gasa da ke gabanta.
Manazarta harkar kwallon kafa sun zaku su ga ko wata daga cikin kungiyoyin za ta nuna gajiyawa bayan kukan kurar da suka yi har suka samu isa semi final a Gasar Zakarun Turai, wato Champions League.
Manazarta irin su Graham Searles, marubuci kan wasanni a jaridar The Guardian ta Burtaniya, na ganin tunzurin da Man City ta yi bayan jerin kashin da ta kwasa a baya ka iya sa kungiyar ta dan yi la’asar, ko da yake hangen martabar da nasara za ta kawo mata ka iya zaburar da ’yan wasanta su tattara hankali a kan manufar da ke gabansu ba tare da an kai ruwa rana ba.
Idan haka ta faru kuwa, to fargabar Tuchel za ta karu kasancewar har yanzu lalube kocin na Chelsea yake yi idan ana batun samo zakakuran ’yan wasan gaba.
Ku yaya kuke kallon wannan wasa? Ku ziyarci shafinmu na Facebook don bayyana ra’ayoyinku.