✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Carabao: Man United za ta hadu da Man City, Leicester City ta gwabza da Aston Billa

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) ta fitar da jadawalin wasan kusa da na karshe (Semi Fainal) na gasar cin Kofin Carabao da aka fi…

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) ta fitar da jadawalin wasan kusa da na karshe (Semi Fainal) na gasar cin Kofin Carabao da aka fi sani da Kofin Carling.

Jadawalin ya nuna kulob din Manchester United zai kara da Manchester City a ranar Talata 6 ga Janairu mai zuwa, yayin da  ranar Laraba 8 ga Janairu 2020 kulob din Leicester City zai kece raini ne da na Aston Billa.

Sai wasanni karo na biyu za a yi su ne a ranakun Talata 28 ga Janairu a tsakanin Aston Billa da Leicester City yayin da a ranar Laraba 29 ga Janairu za a hadu  a tsakanin Manchester City da Manchester United, inda kungiyoyi biyu da suka samu nasara a wasannin biyu za su haye wasan karshe wato fainal.

Kulob din Manchester City ne ya lashe kofin sau biyu a jere inda yake hankoron lashe na  uku a wannan karo.