Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo kan karagar mulki a karo na biyu a ranar 29-05-15, a zaman shugaban kasa na farar hula, wasu `yan kasa da kungiyoyi da ma `yan siyasa suke ta kiraye-kiraye gare shi akan lallai sai gwamnatinsa ta dawo da shirin Yaki da Rashin da`a da gwamnatinsa ta mulkin soja 1984 zuwa Augustar 1985 ta yi amfani da shi wajen kokarin gyara zukatan `yan kasar nan, bisa ga irin yadda `yan kasar suke ganin tarbiyya da kyawawan halaye na zamantakewa da mu`amala tsakanin mutum da mutum sun tabarbare.
Ko zai yiwu a dawo da yaki da rashin da’a (WAI)?
Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo kan karagar mulki a karo na biyu a ranar 29-05-15, a zaman shugaban kasa na farar hula,…