✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 5

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko…

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu

zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram

domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya

magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin

da mutane suka ce, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Ba za a iya a mako shida ba – Hadiza Ahmad
Hadiza Ahmad Babale: “Batun gaskiya shi ne, babu yadda za a yi a iya

magance matsalar Boko Haram a cikin makonni shida saboda abu ne da

yanzu shekara shida an kasa magancewa sai a makonni shida ne za a iya

magance ta? Ina ganin cewa yaudarar al’umma kawai ake so a yi. Ni

shawarata kawai ga ’yan Najeriya ita ce, su dogara ga Allah, su

dukufa wajen yin addu’oi ne mafita ba gwamnatin Najeriya ba.”