✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida?

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko…

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu

zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram

domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya

magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin

da mutane suka ce, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Ba za su iya ba
– Tahir Zubairu
Ustaz Tahi Zubairu: “A gaskiya sojoji ba za su iya murkushe ’yan Boko

Haram a cikin makonni shida kadai ba. Domin idan har za su iya yin

maganin ta’addancin Boko Haram a cikin makonni shida, to me ya hana

su yin hakan a cikin shekaru shida da aka yi ana kashe bayin Allah?

Ina ganin akwai wani boyayyen abu ne da suka kulla a tsakaninsu da

suke so su yi amfani da wannan dama domin cin ma burinsu.”