A kwanakin baya ne Minista Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta maido da harajin hanya a Najeriya. Abin tambaya shi ne, shin ya dace a dawo da wannan haraji ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:
Ya dace a dawo da harajin hanya – Alhassan Muhammad
Abbas Ibrahim dalibi, a Abekuta
Alhassan Muhammad Hassan: “Hakan yana da kyau, domin ban da kudin shigar da gwamnati za ta samu don a gyara hanyoyi, hakan zai samar da ayyukan yi, zai kuma kawo alfanu da dama. Fatanmu dai kawai a sanya kudin da za a samu a inda suka dace, koda yake ba ma tababar hakan; domin wannan gwamnatin ba ta wandaka ba ce.”
Harajin hanya ya dace – Muhammad Bello
Abbas Ibrahim dalibi, a Legas
Muhammad Bello Yusuf: “Hakika ya dace a yi hakan, domin a yanzu Najeriya na cikin halin bukatar kudi, maido da harajin hanya zai ba gwamnati damar samun kudaden shiga, wadanda za su isa a gyara hanyoyinmu, har ma a yi wasu ayyukan kamar gina asibitoci da makarantu kuma mu direbobin manyan motoci; maido da biyan harajin hanya zai kara ba mu kariya ta fuskar tsaro.”
Harajin hanya bai kamata ba – Aminu Usman
Muhammad danladi Ibrahim, a Minna
Aminu Usman dakingari: “Gaskiya wannan matakin da ake maganar dawo da shi, ko kadan bai kamata ba ta kowace fuska. Dalilina shi ne, an bullo da irin wadannan hanyoyi daban-daban da sunan yi wa jama’a aiki, domin biya musu bukatu daban-daban, daga bisani sai a canja wa lamarin akala baki daya. ’Yan Najeriya sun amince cewa Shugaban kasa mai adalci Muhammadu Buhari zai dora kasar nan a turbar da ta kamata, domin ta goga kafada-da-kafada da sauran kasashen duniya, inda suke gayyatarsa suna ji daga bakinsa irin abubuwan da kasar ke bukata. Ni a ganina, wadansu mutane ne suke so su yi amfani da wannan hanyar domin a takura wa wadanda suka zabe shi domin ya fara bakin jini tun yanzu, don a bata masa damar sake tsayawa takara a shekarar 2019 karya suke. Koda za a bullo da irin wannan al’amarin, a tabbatar hanyoyin kasar nan suna da kyau, sannan a fadakar da jama’a muhimmancin yin haka.”
Dawo da harajin bai dace ba – Mannir Musa
Muhammad danladi Ibrahim, a Minna
Mannir Musa Garima Minna: “Ra’ayina game da wannan lamarin na dawo da harajin hanya ko kadan a wannan lokacin da muke ganin alamun canji a al’amura, yadda ake gudanar da al’amuran Najeriya bai dace ba. Jama’a na cikin wani mawuyacin hali da kuma kuncin rayuwa. Babban abin takaici, shi ne wadanda za su kula da al’amarin baki daya za su yi amfani da wannan damar domin azurta kansu. Na yi imani cewa idan aka bayar da risidan da za su ba masu motoci, ba duka za su bayar ba, don kuwa wasu masu ababen hawan ba kudin da aka kayyade za su bayar ba. Ka ga irin wadannan ba za su amshi risidin ba. Ko kuma idan risidan suka kare, ba za su fito da wata kafa ta rubuta kudi da kuma abin da ya danganci haka ba.”
Ya dace a biya harajin hanya – Abubakar dandada
Hamza Aliyu, a Bauchi
Abubakar dandada: “To idan an ce haraji wani kudi ne da ake sa wa ga ’yan kasuwa da ma’aikata. A shekarun baya kudin haraji ya yi tasiri sosai wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, za ka ba da Naira 20 amma za a yi maka aiki sama da Naira 100. To idan haka ne, yana da kyau a ci gaba da karbar kudin harajin hanya a Najeriya.
Kamar yadda Minista Babatunde Raji Fashola ya fadi cewa masu motoci za su fara biyan haraji domin gwamnati ta samu kudin da za ta shimfida ayyukan alheri ga ’yan kasa, ina goyon bayan wannan mataki dari bisa dari. Kuma ya kamata a fahimci cewa biyan haraji ba wani sabon abu ba ne, shugabannin baya sun yi watsi da batun ne. Sannan abin da ya sa wasu ke kin biyan haraji shi ne, wasu lokutan mutane za su biya makudan kudi amma daga bisani sai ka ga kudin ba su shiga asusun gwamnati ba. Ina tabbatar wa al’umma da masu motoci su biya kudin domin Shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana kuma za a yi aiki da kudin da aka karba ta hanyoyin da suka kamata.”
Na goyi bayan harajin hanya – Abdallah Caps
Hamza Aliyu, a Bauchi
Abdallah Caps: “Abin da zan fada game da wannan tambaya shi ne, ina goyon bayan maganar da Minista Fashola ya yi cewa masu amfani da motoci za su fara biyan harajin hanyoyi; domin gwamnatin ta yi alkawurra masu yawa ga al’umma. Da yawa daga cikin hanyoyin Najeriya da masana’antu da makamantansu da kudin haraji aka gina, don haka biyan haraji ya zamo kusan wajibi a kan masu motoci. Kowace gwamnati tana zuwa da sababbin manufofinta kuma ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa, gwamnatin Buhari babban abin da yake gabanta shi ne inganta rayuwar kowa da kowa kuma idan an fara biyan kudin harajin hanya talaka ne zai fara amfana. Daga karshe muna fatar Allah Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda za su yi tirjiya wajen biyan kudin su fahimci gwamnatin APC ta sha bamban da gwamnatocin baya.”