✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a hana shigo da kananan janaretoci a Najeriya?

A kwanakin baya, an fara cewa za a haramta shigo da kananan janaretoci cikin Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a…

A kwanakin baya, an fara cewa za a haramta shigo da kananan janaretoci cikin Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a dauki wannan mataki ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Bai da ce a hana shigo da su ba – Bature Yango

Hussaini Isah, a Jos

Alhaji Bature Yango: “Gaskiya bai dace a hana shigo da kananan janaretoci kasar nan ba, domin wadannan kananan jannareta suna taimaka wa matasan kasar nan wajen gudanar da sana’o’insu, don rike kansu da iyalansu a birane da kauyuka. A kullum ana cewa a samar wa matasa ayyukan yi, don haka wannan mataki da ake son dauka bai dace ba. Duk da cewa wutar lantarki ta fara samuwa a kasar nan, amma har yanzu wannan wuta ba ta gama tsayawa ba. Kuma akwai kauyuka da dama da ba su da wutar lantarki baki daya a kasar nan. Don haka idan aka dauki wannan mataki, to Allah ne kadai Ya san yawan matasan da za su rasa aikin yi a kasar nan. Idan an ce irin wadannan kananan  janareta suna gurkata muhalli, sai a kawo abubuwan da za a maye gurbinsu da su, kamar irin kananan injinan bayar da wuta masu aiki da hasken rana, kafin a ce za a dauki wannan mataki.”

Ya dace a hana shigo das u – Manu Idris

Hussaini Isah, a Jos

Malam Manu Isah Idris: ‘’A gaskiya hana shigowa da kananan janaretoci zuwa kasar nan da gwamnati take son ta yi ya yi daidai, domin irin wadannan kananan injina suna gurkata muhalli da kawo dumamar yanayi a kasar nan, ta hanyar hayakin da suke fitarwa. Yanzu sakamakon irin wannan matsala akwai rafuka da dama da suka kone a kasar nan, wanda wannan zai iya kawo wa harkokin noma cikas. Don haka wannan mataki da gwamnati take son dauka, na hana shigo da kananan janaretoci abu ne mai kyau. Duk kasashen duniya abin da ake ta magana ke nan, wato matsalar dumamar yanayi da gurkacewar muhalli, wanda hayakin da injinan suke fitarwa yake kawowa. Don haka ina jan hankalin masu amfani da irin wadannan kananan janaretoci  su yi hakuri, kuma su fahimci cewa wannan gwamnati za ta dauki wannan mataki ne domin kare lafiyarmu. Kuma  tana nan tana kokarin gyaran wutar lantarki. Idan aka kammala wannan aiki, za a samu wadatacciyar wutar da za ta maye gurbin wadannan kananan janaretoci.”

Ya dace a hana idan… – Abdullahi Usman

Abubakar Haruna, a Abuja

Abdullahi Usman: “A ra’ayina idan gwamnati za ta wadata kasa da wutar lantarki, to ina goyon bayan a dakatar da shigo da janaretoci amma idan gwamnati ba za ta samar da wutar lantarki ba to bai dace ta dakatar da shigo da injinan ba.”

Bai dace ba – Shamsuddin Abdullahi

Abubakar Haruna, a Abuja

Shamsuddin Abdullahi: “Ni a ra’ayina, ina ganin bai dace ba saboda ba mu da wadatacciyar wutar lantarki, don haka idan gwamnati ta hana shigo da janaretoci to babu shakka mutane za su shiga halin kaka-ni-kayi; don har yanzu da injin janareto ake dogara a wurare da yawa a kasar nan.”

Bai dace a hana shigo da su ba – Aliyu Muhammad

Shu’aibu Ibrahim Gusau, a Gusau

Aliyu Muhammad: “Bai dace gwamnati ta hana shigo da kananan janareta ba saboda har yanzu gwamnati ba ta magance matsalar wutar lantarki da ake fama da ita ba, duk da yadda ake raba wuta tsakanin unguwanni. Wadannan kananan janaretoci ne ke share wa jama’a hawaye don su ne masu saukin kudi, da koda kananan ’yan kasuwa su suke amfani da su, don haka idan gwamnati za ta yi haka sai ta waddata jama’a da wuta da wadatattun tiransifoma da ake rarraba wutar da su.”

Ya dace a hana shigo da su ba – Abubakar Ibrahi

Shu’aibu Ibrahim Gusau, a Gusau
Abubakar Ibrahim: “Ni a ra’ayina, ya dace gwamnati ta hana shigo da janareta, domin idan ta hana shigo da su to ya zama wajibi ta samar da wutar lantarki wadatacciya, domin al’umma za su fi samun sauki dangane da abin da ya shafi wuta kuma yawan janareta yana taimakawa wajen gurkacewar yanayi.”