Tsakanin Talata da Alhamis makon da ya gabata 9 da 11-07-14, wasu jaridun kasar nan ciki har da `ya`yar wannan jaridar Daily Trust, sun cika da tallace-tallace na wasu kungiyoyin Jam`iyyar PDP, rassan jihohin Bayelsa da Barno da suka shiga cece-kuce akan cancanta da rashin cancantar uwar jam`iyyarsu ta kasa baki daya ta karbi tsohongwamnan jihar Barno Sanata Ali Modu Shariff, wanda ake wa lakabi da SAS, bisa ga sabuwar aniyarsa ta ya canja sheka daga jam`iyyar APC zuwa PDP, mai gwamnatin tsakiya.
Sanata Ali Modu Shariff ya ci zabe, ya kuma zama dan Malisar Wakilai ta tarayya a jamhuriya ta uku ta tsohon shugaban kasa na mulkin soja janar Ibrahim Babangida (1992 zuwa 1993), wadda ba ta kai labari ba. Tauraruwar siyasarsa ta fara haskawa ne a cikin siyasar jiharsa ta Barno a wannan jamhuriyar da muke ciki, lokacin da ya zama uba ga duk wani mai son dana madafun iko a jiharsa ta Barno, to kuwa sai da goyon bayansa zai kai labari, hatta Gwamna Alhaji Kassim Shettima mai ci yanzu, wanda ya gaji Sanata Ali Modu. Tauraruwarsa ta haska fayau a shekarar 2003, lokacin da yake dan Majalisar Dattawa a jam`iyyarsu ta APP, inda ya raba Gwamnan jihar Alhaji Malah Kachallah da jam`iyyar, ya kuma yi mata takarar gwamnan jihar, ya kuma kada gwaman mai ci da ya koma jam`iyyar AD.
Tun a shekarar 2011, shekarar karshe ta zango na biyu na mulkin Sanata Ali Modu Shariff, na shekaru 8, 2003 zuwa 2011, ake ta rade-radi bisa ga take-takensa da maganganunsa na nuna goyon baya ga gwamnatin tarayya ake ta zargin gwamnan na Barno, zai yi canjin sheka, amma dai hakan ta kasa tabbata, a lokacin da ya dage ya tabbatar da cewa jam`iyyarsu ta ANPP, ta sake rike kambinta na ci gaba da mulkin Jihar Barno a karkashin jagorancin dan takararta Alhaji Kassim Shettima, a shekarar 2011 din.Yanzu ma wadannan rade-radi suka sake kunno kai a daidai lokacin da guguwar zabubbukan 2015, ta fara kadawa.
Rahotanni sun tabbatar zuwa yanzu, tun a wajen wancan babban taron farko na kasa baki daya na jam`iyyar APC, wanda aka yi a Abuja ranar 13-06-14, inda a karon farko aka zabi sababbin shugabanninta na kasa baki daya, aka ce tsarin yadda aka yi zabubbukan ko kusa ba su yi wa Sanata Ali Modu dadi ba, ba don komai ba, sai don irin yadda wai an kai masa wa aka ci ka tashi, lokacin da wasu iyayen jam`iyyar ciki kuwa har da yaronsa, kuma gwamnan jiharsa, Alhaji Kassim Shettima, wadanda suka yi kutu-kutun kar a zabi Alhaji Kassim Imam,wanda shi Sanata Modu Shariff yake mara wa baya a matsayin Babban Sakataren Jam`iyyar, maimakonsa sai mutane irin su gwamnonin jihohin Barno da Yobe suka mara wa Alhaji Tijanni Musa Tumsah baya daga jihar Yobe, wanda kuma dama shi ne Sakataren riko na Jam`iyyar.
Wannan canjin sheka Sanata Ali Modu ya riga ya yi, ba wani sabon labari ba ne daga abin da hadakar wadancan jam`iyyu ta haifar, don kuwa tuni tsofaffin gwamnonin jihohin Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa da na Kano Malam Ibrahim Shekarau suka canja sheka daga APC zuwa PDP, har ma PDP din ta yi wa Malam Shekarau Ministan Ilmi, yayin da shi kuma Alhaji Baffarawa yake jiran wani gundumemen mukami a zaben 2015. Inda yake sabon labara, shi ne irin jijiyar wuya da wasu magoya bayan shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da na SAS kan kar a karbe shi, da kuma lalle sai PDP ta karbe shi.
`Yan kunngiyar kariya da goyon bayan takarar shugaban kasa ta 2015, wadanda kuma suke `yan asalin jiharsa ta Bayelsa mai suna Bayelsans Adbocacy and Defence Round Table ta buga wata talla a yayar wannan jaridar ta ranar Talata 09-07-14, inda ta shawarci Alhaji Ahmed Mu`azu Shugaban Jam`iyyar PDP na kasa baki daya da dukkan sauran shugabannin jam`iyyar masu fada a ji, da kada su kuskura su amince da canjin shekar ta tsohon gwamnan na Barno zai yi zuwa PDP din. Mutanen biyu da suka sa hannu akan koke-koken, wato Mista Inemo Ebiere da Mista Smith Tamarauemi, shugaba da mataimakin Sakataren kungiyar bi da bi, duk sun ta`allaka hujjojinsu akan zargin Sanata Ali Modu shi ne kanwa uwar gami, kuma yana da hannu dumu-dumu a cikin kafuwa da ruruwar rikicin `yan kungiyar Jama`atu Ahlis sunnah Lid da`awati Wal Jihad, wato Boko Haram da aka fara a Maiduguri tun a shekarar 2009, lokacin yana mulki. Suka ce babbar fargabarsu wannan rikici na Boko Haram zai iya zama wani babban batun yakin neman zaben 2015, ta yadda dansu ka iya rasa cin zaben.
Shi kansa Sanata Ali Modu ya sha nisanta kansa akan yana da hannu cikin rikicin na Boko Haram. Yanzu kuma sai ga wata kungiya mai goyon bayansa ta fito da ta ta kariyar, kungiyar mai suna Borno Intergrity Initiatibe, wadda ta sa talla a jaridar Daily Trust ta ranar Alhamis da ta gabata, bayan ma ta nisanta tsohon gwamnan ta kuma kafa hujjarta da cewa ai yana daga cikin wadanda rikicin na Boko Haram ya jikkaka, don kuwa har kanensa da abokan siyasarsa na kut-da-kut aka kashe a cikin rikicin, inda take nisanta tsohon gwamnan, sannan ta yi kira ga jam`iyyar PDP da ta gaggauta karbarsa.
A irin yadda rikicin nan na Bako Haram ya-ki-ci-ya ki cinyewa, wanda kuma yana ta ta`zzara ne akan rashin shugabanci mai cike da adalci, Ina ga bai kamata batun canjin shekar tsohon gwamnan ta zama wani abin cece-kuce ba, ba don kome ba, sai don samun zaman lafiyar kasar nan shi ya fi kome muhimmanci. Akwai babbar fargaba matuka akan makomar tsaro da zamantakewar kasar nan, don haka ya zama wajibi ga masu mulki da masu neman mulki, tun daga sama har kasa, su rika takatsantsan akan dukkan abin da za su aikata, ko su sa a aikata. Allah Ya yi mana jagora.
Ko PDP ta amince da gargadin da aka yi mata kan SAS?
Tsakanin Talata da Alhamis makon da ya gabata 9 da 11-07-14, wasu jaridun kasar nan ciki har da `ya`yar wannan jaridar Daily Trust, sun cika…