Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook.
- Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro
- Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC
“Gaskiya ne na koma APC. Damuwata a ko yaushe ita ce walwalar al’ummar mazaɓata,” in ji shi.
Sanatan ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na sauya sheƙar ya yi shi ne domin inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa, da kuma tabbatar da ci gabansu mai dorewa.
Kawu dai ya daɗe da raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da NNPP da ya yi takara ƙarƙashin ta, wanda ya sanya wasu da dama suka daɗe da hasashen zai sauya sheƙa zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC da ya bari a wancan lokacin.