✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ko kwalliyar Chelsea za ta biya kudin sabulu a Gasar Zakarun Turai?

Chelsea ta kashe kudi mai yawa wajen daukar sabbin ‘yan wasa kuma da dan karen tsada.

Chelsea za ta fafata da Borussia Dortmund a wasa na biyu a Gasar Zakarun Turai, zagayen ’yan 16 da za su kara a Stamford Bridge ranar Talata.

Karo na biyu da za su yi tata burza a Gasar Zakarun Turai, inda Dortmunt ta ci 1-0 a Jamus a ranar 15 ga watan Janairu.

Chelsea dai na fama da kalubale, tun bayan da ta sallami kociyanta, Thomas Tuchel ta dauki Graham Potter, wanda bai san dadin Gasar Zakarun Turai ta Champions League ba.

Chelsea ta kashe kudi mai yawa wajen daukar sabbin ‘yan wasa kuma da dan karen tsada musamman lokacin da aka bude kasuwar musayar ’yan kwallo a watan Janairu, amma tana ta 10 a teburin Firimiyar Ingila.

Ana sa ran Reece James da Cristian Pulisic sun murmure, yayin da Thigo Silva ke jinya, an dakatar da Mason Mount.

Shi kuwa mai tsaron ragar kungiyar Jamus, Gregor Kobel, watakila yana da koshin lafiya tare da Donyell Malen.

Sai dai Karim Adeyemi na jinya, shi ne ya zura kwallo a ragar Chelsea a Jamus, yanzu rabon ya taka leda tun 19 ga watan Fabrairu.

Bayan wannan wasan Chelsea za ta buga Firimiyar Ingila da Leicester City ranar 11 ga watan Maris a King Power.

Dortmund wadda take ta biyu a teburin Bundesliga, za ta ziyarci Schalke a gasar Bundesliga ranar Asabar 11 ga watan Maris.

%d bloggers like this: