✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko gudanar da zabubbuka zai kawo karshen rikicin da APC ta shiga?

Yanzu dai ta tabbata kwamitin zartarwa na kasa baki daya na jam`iyyar APC, mai mulki da gwamnatin tsakiya ya ba bori kai ya hau dangane…

Yanzu dai ta tabbata kwamitin zartarwa na kasa baki daya na jam`iyyar APC, mai mulki da gwamnatin tsakiya ya ba bori kai ya hau dangane da amincewar da ya yi na gudanar da zabubbukan shugabannin jam`iyyar tun daga sama har kasa, har ma ya mikawa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wa`adi kwan 21, wanda ya ke cikin sharuddan yin zaben. Ana kuma sa ran zuwa lokacin da mai karatu yake karanta wannan makala, jam`iyyar ta fitar da jadawalin irin yadda tsarin zabubbukan za su kasance, da ma wanda zai shugabanci kwamitin babban taronta na kasa da ake ta kishi-kishin din Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar Gwamnan Jihar Jigawa zai shugabanci Kwamiti. An ta dai kai ruwa rana tsakanin 27 ga watan Fabrairun da ya gabata zuwa 27 ga watan Maris din da ya gabata akan makomar shugabannin jam`iyyar tun daga sama har kasa da wa`adinsu zai kare a ranar 30-06-18, kafin cimma wannan matsaya. 

Ana cikin rudanin cancanta da rashin cancantar yin karin wa`adin shekara daya ga zababbun ne, da har wasu `yan jam`iyyar suka garzaya kotu suna kalubalantar yin sa. Kwatsam!  sai aka jiyo Shugaban kasa Muhammadu Buhari a faffadan taron jam`iyyar ta APC na ranar 27-03-18, a cikin jawabinsa ya fito karara, ya soki karin wa’adin, harma yana kafa hujja da cewa sassa na 17 (1) da 13.2 (B) na kundin tsarin mulkin APC ya kayyade wa’adin shugabannin da aka zaba ne zuwa shekara 4, wanda kawai za a iya ci gaba ne ta hanyar sake wani sabon zaben, yayin da sashe na 223, na kundin tsarin mulkin kasa na 1999, ya fayyace dukan matakan zabubbukan shugabanni a kowane mataki bai wuce shekara hudu. Zama a kan Kwamitin riko in ji shugaba Buhari zai iya ma haramta `yan takarar da jam`iyyar za ta fitar don yi ma ta takarar zabubbukan badin.

Duk da wancan jawabi na shugaba Buhari, shugabancin jam’iyyar na APC na kasa baki daya bai karbesu da zuciya daya ba, har sai da ya kafa wani kwamiti da ya kira na kwararru a karkashin jagorancin gwamnan Jihar Filato Mista Simon Bako Lalong da ya dora wa alhakin bin ba’asin jawabin shugaban kasar,sannan ya ba jam’iyyar shawara akan abin da zai zama mafita a dambarwar da ta fada akan yin zabubbukan ko kara wa’adin.

Kwamitin kwararrun na gwamnan Jihar ta Filato, tuni ya fitar da rahotonsa, inda ya bada shawarwarin da su ka hada da lalle Jam`iyyar ta APC ta gaggauta gudanar da tarurrukanta tare da zaben sabbin shugabanni tun daga sama har kasa. Kwamitin kuma ya bada shawarar a zauna akan tsarin da ake kai yanzu na raba mukamai a zaman shiyya shiyya, a babban zaben shugabannin na kasa baki daya, sannan dukan `yan jam`iyyar da suka gurfanar da jam`iyyar gaban kuliya akan wancan karin wa`adi da su gaggauta janye kararrakin. Mai karatu kar ka manta cikin wancan dambarwa sai da gwamnonin APC suka yi taro da shugaba Buhari, taron da a lokacin ba a cimma wata matsaya ba akansa, har sai washe gari, bayan wasu daga cikin gwamnonin sun sake komawa sun ga shugaba Buhari kana gwamnoni 20 daga cikin gwamnonin APC 24, suka fitar da wata sanarwa a Abuja suna neman da lalle a manta da batun karin wa`adi a gudanar da zabubbuka kawai.

Tun kafin akai ga wannan matsayi a gefe daya, akwai rahotanni masu karfi da suke nuni da cewa tuni a cikin jam’iyyarta APC ake rade-radin tsohon gwamnan Jihar Edo Kwamared Adam Oshiomhole da tsohon shugaban jam’iyyar APP kuma wanda ta fara fitarwa da farko a zaman dan takararta cikin neman shugabancin kasa, yanzu kuma Ministan Kimiyya da Fasaha Dokta Ogbonnaya Onu da kuma tsohon shugaban Majalisar Dattawa kuma tsohon dan jam’iyyar PDP kuma shugaban Kwamitin gyaran harkokin zabe Mista Ken Nnamani, suke kan gaba wajen wanda zai gaji Mista Oyegun a zaman shugaba, koda yake yanzu kwamitin gwamna Lalong ya bada shawarar a bar kowane mukami a shiyyar da yake, in har haka ta tabbata Kwamared Oshiomhole da ya fito daga shiyya daya da Cif Oyegun wato Kudu maso Kudu ke nan shi ke da dama sama da sauran `yan takarar neman shugabancin jam`iyyar na kasa baki daya, sannan dadin dadawa kuma akwai rahotanni masu karfi da suke nuni da cewa shugaba  Buhari da jagoran jam’iyyar APC na kasa baki daya Alhaji Ahmed Bola Tinubu sun hadu akan su na son Kwamared Oshiomhole ya zama sabon shugaba. 

Wannan dambarwa da APC din ta shiga ta irin yadda ake ganin shugaba Buhari da gwamonin jam’iyyar sun dauki matakan kawo karshensu, musamman wajen farantawa Tinubu, da ya dade basu ga maciji da Cif Oyegun, ana ganin hakan zai taimaka wajen kawo karshen rigingimun jam’iyyar, don kuwa, an ji Tinubu yana kalaman madallah tare da jaddada cewa yanzu za a samu sasanta ‘yan jam’iyyar da aka batawa rai, ake kuma neman lalle su hakura, kasancewar shi ke shugaban wancan Kwamiti. 

Amma kuma kada mai karatu ya manta da cewa har yanzu fa ba a ga maciji tsakanin bangaren zartarwa da na Dokoki na kasa, bisa ga irn yadda wasu daga ‘yan Majalisun Dokokin na kasa ciki kuwa har da shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki suke fuskantar tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa gaban kotuna daban-daban. Wannan rashin jituwa ita ta haddasa mutane da dama da shugaba Buhari ya mikawa Majalisar Dattawan sunayensu don neman amincewarta kafin ya nada su mukamai, Majalisar ta jingine batunsu, cikinsu kuwa har da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC, wato Alhaji Ibrahim Magu. Kuma ko a karshen makon da ya gabata an rawaito shugaban Majalisar Dattawan a yayin bude wani taron karawa juna sani ga ‘yan Majalisar a Jos babban birnin Jihar Filato yana cewa sabanin da ke tsakinisu da bangaren Zartaswa zai ci gaba koda ba shi ke kan kujera ba, muddin ba a samun cudanya da hadin kai tsakanin bangarorin biyu. 

A gefe daya kuma kowa ya san cewa yanzu maganar da ake Majalisar Dattawan ta kama hanyar yin amfani da ikonta wajen hawa kujerar naki don zartar da dokar da  ta canja tsarin zabe ta raba hada zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisun Dokokin na kasa, wanda aka saba yi tare tun bayan dawowar wannan  jamhuriya ta hudu a shekarar 1999. Gyaran da ake zargin ‘yan Majalisun Dokokin sun kuduri aniyar yinsa ne saboda shugaba Muhammadu Buhari. A gefe daya kuma ga dambarwar zartar da kasafin kudi da ake fama da ita duk shekara tsakanin bangaren Zartarwar da na Dokoki. 

Da irin wadannan sabani da na gabatar a sama da ma wadanda ban iya gabatarwa ba, ka iya cewa ba yin zabubbukan sabbin shugabannin jam’iyya tun daga sama har kasa cikin jam’iyyar APC za su kawo karshen wadannan rigingimun ba. Don kuwa a duk lokacin da kakar zabe irin wannan ta kunno kai da kuma irin yadda yanzu shugaba Buhari a ranar Litinin din da ta gabata ya bayyana aniyarsa ta zai sake neman wa`adin zango na biyu, ka iya ce rigingimu cikin jam`iyyar APC, ba za su lafa ba, har sai bayan zabubbukan badi in Allah Ya kaimu.