✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ciyar da yara abinci zai bunkasa harkar ilimi?

Zai taimaki yara fahimtar karatu – Shehu Adamu Shehu Adamu Yakasai: “Idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a kasar nan na matsin…

Zai taimaki yara fahimtar karatu – Shehu Adamu

Shehu Adamu Yakasai: “Idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a kasar nan na matsin tattalin arziki, babu shakka ciyarwar da gwamnatoci ke yi a makarantu za ta bunkasa harkar ilimi. Mafi yawan ’ya’yan talakwa suna tafiya makaranta ba tare da samun wani isasshen abinci ba. Kowa ya san ilimi ba zai samu da yunwa ba. Idan yaran suka sami wannan abincin, za a iya samun nasara, dalibi ya mayar da hankali ga abin da ake koya masa.”

Ciyar da yara na da amfani – Abdullahi Ahmad

Lubabatu I. Garba, a Kano

Abdullahi Ahmad: “Ciyarwar tana da amfani matuka, yawancin ’ya’yan da ke makarantun gwamnati ’ya’yan talakawa ne, wadanda za ka samu suna zuwa makaranta ba tare da kudin kashewa ba. To, wannan abincin suke samu su ci, wanda kuma yakan taimaka su fuskanci karatun da malamansu ke koya musu. Ni kaina ina da ’ya’ya biyu da ke makarantar firamare, muna jin dadin hakan da gwamnati ke yi. Fatanmu shi ne gwamnati ta kara bunkasa al’amarin.”

Ciyarwar ba za ta magance matsalar ilimi ba – Fati Usman

Rabilu Abubakar, a Gombe

Fati Usman Kulani: Ni a ganina, wannan tsari abu ne mai kyau sai dai ba zai magance matsalar ilimi ba amma zai magance matsalar yunwa, wacce na san cewa tana hana yara karatu amma idan akwai malamai masu kwazo; za a iya magance matsalar. Samar da kwararrun malamai da kayayyakin koyarwa su ne za su farfado da matsalar ilimi ba ciyar da dalibai abinci ba. Duk da haka, yana da kyau a ci gaba da irin wannan tsarin, zai taimaka wajen rage yunwa ga su daliban don ta kan hana su samun natsuwa a lokacin karatun.”

Ilimi zai inganta -Sani Sadik

Rabilu Abubakar, a Gombe

Sani Sadik, Makeran Farfarun Gombe: “A nawa ra’ayin, ciyar da dalibai abinci a makarantu zai kara inganta harkar ilimi, domin ana iya samun yaran da sukan tafi makaranta ba tare da sun karya ba balle abincin rana. Ko da manyan kasar nan da suka zama wani abu, ai tun a wancan zamani nasu kyauta suka yi karatu, komai nasu kyauta aka yi musu; shi ya sa suka yi karatu saboda da yawansu ’ya’yan talakawa ne. Ina kira ga sauran gwamnonin jihohinmu da su yi koyi da wannan tsari na gwamnatin Kaduna.”

Ba shi ne matakin ciyar da ilimi gaba ba – Umar Ibrahim

Muhammad Yaba, a Kaduna

Umar A. Ibrahim: “Ciyar da dalibai abinci ba shi ne matakin ciyar da ilimi gaba ba, domin kamata ya yi a samu kwararrun malamai da za su karantar da yara sannan a gyara da kuma gina sababbin ajujuwa da za su dauki yawan daliban da suke makarantun gwamnati. Haka nan akwai bukatar gwamnati ta takaita yawan dalibai a aji saboda malaman su samu damar karantar da yaran da kyau.”

Ciyarwar za ta taimaka amma… – Bello Dallaji

Muhammad Yaba, a Kaduna

Bello Idris Dallaji: “Ciyarwa ba shi ne matakin inganta ilimi ba amma dai zai taimaka domin su yaran da suke zuwa makarantun gwamnati, yawancinsu ’ya’yan talakawa ne saboda haka abincin da ake ba su zai ja ra’ayin iyayensu wajen tura su makarantar nan, don samun ilimi. Iyayen suna ganin an taimaka masu wajen dauke masu nauyin ciyar da ’ya’yansu abinci sau daya. Gaskiya hakki ne a kan gwamnati ta inganta makarantu domin a yanzu yaran nan a kasa suke zama yayin daukar karatu.”