✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ko Arewa24 sun nemi in dawo Kwana Casa’in ba zan dawo ba –Safara’u

Yadda na fara fim daga rakiya da abin da dalilin barina Kwana Casa'in

Safiyya Yusuf, wadda aka fi sani da Safara’u Kwana Casa’in fitacciyar matashiyar jaruma ce a shirin Kwana Casa’in da ake haskawa a tashar Arewa24.

An daina ganinta a tsakiyar shirin, wanda hakan ya sa masu kallon shirin ke tambayar me ya sa.

A zantawarta da Aminiya, ta bayyana yadda ta fara fim daga rakiya, da Kwana Casa’in da sauransu.

Ki fara da gabatar mana da kanki.

Sunana Safiyya Yusuf, ni ’yar asalin Jihar Kano ce, kuma ni Bafulatana ce.

Na yi firamare a garin Ibadan, inda na taso har zuwa lokacin da na kai shekara 11 domin mahaifina soja ne.

Sannan na yi sakandare a Nasara Academy da ke Kano.

Yanzu haka ni jarumar fim ce, sannan ina kasuwanci. Wannan ke nan a takaice.

Yaya aka yi kika fara fim?

Mukaddari ne kawai. Na fara fim ne daga rakiya. Ban taba tunanin zama ’yar fim ba. Ko kadan ba ya cikin lissafina.

Kwana Casa’in ne fim dina na farko.

Yadda abin ya faru shi ne, watarana wata kawata mai suna Maryam Malumfashi ta zo ta ce in raka ta, za ta je wajen da ake gwada jarumai da za a yi fim din Kwana Casa’in da su.

Da muka je wajen, sai kuma ta ce mu shiga tare, domin a cewarta, za ta fi natsuwa idan muna tare. Shi ke nan fa, sai muka shiga tare.

Da muka shiga aka gwada, cikin ikon Allah sai na samu, amma ita ba ta samu ba.

Ita ce ke da sha’awwa, amma ni daga rakiya sai na aka dauke ni. Ka ji yadda na fara fim.

Mene ne burinki yanzu da kika fara fim din?

Ina da burika da yawa gaskiya. Ina da burin zama furodusa a masana’antar Kannywood, sannan ina so in zama darakta a nan gaba. Gaskiya zan so hakan ya faru.

Ba ma a Kannywood kadai ba, har da Nollywood na Kudu. Ina son finafinan Nollywood sosai.

Wane shiri kike yi na zama furodusa ko darakta?

A gaskiya ba wani shiri da nake yi a yanzu. Ni dai na san ina da burin hakan.

Don haka kawai ina jiran lokaci ya yi ne, domin komai yana da lokacinsa.

Amma lallai ina da sha’awar bangaren.

Za ki iya fitowa a fina-finan Kudu?

Zan iya fitowa mana amma sai dai a matsayina na Musulma, dole akwai abubuwan da ba zan iya yi ba.

Akwai abubuwa irinsu sanya matsattsun kananan kaya da sauransu.

Amma ina da sha’awar fina-finan Nollywood gaskiya kuma idan lokaci ya yi kuma na samu dama, zan yi.

Bari mu dawo bangaren da aka fi saninki. Wace rawa kika taka a shirin Kwana Casa’in?

A Kwana Casa’in na fito ne a matsayin wata matashiya da take son karatu. Mai ladabi da biyayya.

Burina shi ne in yi karatu sosai, in zama likita domin in yi wa mahaifiya magani kasancewar tana da ciwo a kafa.

Sannan ina da buri na zama likita in taimaki mutane.

Amma shi mahaifina ba ya son in yi karatu, ya fi son ya min aure domin shi kudi kawai yake so saboda mu talakawa ne a fim din.

Bayan an daina ganin ki a shirin Kwana Casa’in, masu kallo sun rika cewa sun fi son a dawo da ke, yaya kika ji a lokacin?

Na ji dadi sosai, a wani bangaren kuma ban ji dadi ba.

Abin da ya sa na ji kuwa shi ne, jin yadda mutane suke yabo na, suna cewa ba sa son sabuwar Safara’un da aka kawo.

Ba wai ina cewa ni ba na son sabuwar Safara’un ba ce, a’a, ina fadan abin da mutane suka fada ne, kuma gaskiya na ji dadi.

Sannan a dayan bangaren kuma na ji haushin rashin samun damar ci gaba da shirin.

Abubuwa da dama sun faru, sannan an samu wasu sabani har ta kai ga abin da ya faru. Ana ta maganganu a kan asalin abin da ya sa aka daina ganinki a shirin, mene ne asalin dalili?

Lokacin da ake ci gaba da daukar shirin ne na kwanta rashin lafiya.

Sun fara aiki, ni kuma ina kwance ba ni da lafiya, don haka ne a lokacin suka ga ba za su iya jira na ba, sai suka dauko wata ta ci gaba a matsayina domin a gaskiya a lokacin ba zan iya yin aiki ba domin ba ni da lafiya sosai.

Tun bayan Kwana Casa’in sai aka ji ki shiru, kin bar fim ne?

A’a. kwanan nan na dawo daga Kaduna, inda na je wani aikin. Sunan fim din Kaddarar So. Shi ma mai dogon zango ne.

Don haka har yanzu ina fim, kuma nan ba da jimawa ba masoyana za su gan ni a fim din, kuma zai nishadantar da su matuka.

Ke nan ba ki yin fim sai mai dogon zango?

Ba haka ba ne. Ina yin kowane fim. Amma gaskiya na fi son fina-finai masu dogon zango.

Amma hakan ba yana nufin ba zan iya yin fina-finai kanana ba. Zan yi kowane iri ne.

Kina kewar fim din Kwana Casa’in?

Eh, dole ina kewar shirin gaskiya, musamman yadda muke daukar shirin cikin jin dadi tare da abokan aikina da furodusoshi da daraktoci da sauransu.

Gaskiya nakan yi kewar shirin.

Idan aka bukaci ki dawo a ci gaba da ke, za ki amince?

Eh, zan so in koma, amma gaskiya ba zan iya ba.

Sun riga sun canja ni da wata Safara’un, sannan idan suka ce za su sake dawo da ni, ba karamin asara za su yi ba.

Don haka, duk da cewa ina kewar shirin, ko sun bukaci in dawo ba zan dawo ba.

Amma masoyanki za su so ki dawo

Na sani, kuma zan so in musu abin da suke so, amma tunda lokacin da nake rashin lafiya suka kasa jira na, suka canja ni da wata suka ci gaba da shirin, kawai su cigaba da wadda ta canje ni din.

Gaskiya ba zan iya komawa ba.

A masana’antar Kannywood su waye kike kallo a matsayinki madubinki?

A mata gaskiya gwanayena su ne Rahama Sadau da Hadiza Gabon.

Gaskiya ina kaunar mutanen nan har cikin zuciyata.

A maza kuma gwanayena su ne Ali Nuhu, sai Yakubu Mohammed sai Sani Danja.

Wane sako kike da shi ga masoyanki?

Ina kira gare su da kara hakuri da ni.

Ba za su kara gani na a Kwana Casa’in ba, amma za su ci gaba da gani na a wasu fina-finan.

Su tsimayi sabon fim dina Kaddar So, ina yakinin zai kayatar da su matuka.

Ina godiya matuka da kaunar da suke nuna min.

Yaya za ki kwatanta Safara’un Kwana Casa’in da Safiyya a gida?

A shirin Kwana Casa’in, na fito ne a matsayin matashiya wadda magana ma bai dame ta ba. Kawai karatuna ne a gabana.

Amma a zahiri gaskiya, ina son nishadi. Na fi zama da mahaifiyata a gida, kuma muna yawan hira da ita.

Ina son rawa, da jin wakoki. Yawancin lokuta a Instagram za ka ga ina rawa ko ina jin waka ne.

Amma ba ni da raini ko jijji da kai kamar yadda nake a fim.

Ba na son damuwa. Kawai dai ni mace ce mai saukin kai, mai burin jin dadi da nishadi.

Na fi damuwa da abubuwan da suke gabana.

Kwanaki an ga wani bidiyon tsiraci da aka rika cewa ke ce a ciki, yaya kika ji a lokacin?

Na shiga damuwa sosai, amma ban nuna wa kowa ba, kuma ban ce komai ba.

Abin da ya zo min zuciya shi ne, akwai alamar zan samu daukaka a gaba shi ne hakan ya faru.

Allah ne kadai Ya san kaddara, shi Ya san komai, kuma shi Ya san me ya sa kaddarata ta zo a haka.

Shi Ya sa na yi shiru, na yi ta yin addu’a ga Allah Shi kadai.