Kocin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jürgen Klopp ya bayyana cewa rafali ya yi daidai da ya ba shi jan kati a wasan da kungiyar ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Manchester City.
Klopp ya amince cewa abin da ya aikata a lokacin wasan ya cancanci katin sallamar sa daga filin wasan da rafali Anthony Taylor ya yi ana tsaka da wasan.
- An gano bututun satar mai a kusa da sansanin soji
- Ba zan halarci taron tattaunawa da ‘yan takarar Shugaban Kasa ba —Kwankwaso
“Ni na ja wa kaina jan kati, saboda ta zuwa makatdi da rawa a lokacin, amma ba na nadamar abin da na aikata,” in ji shi.
Ya ce “Idan ka kalli hotunan abubuwan da suka faru a baya, a matsayina na mai shekara 55, na san yadda nake yi a irin wadannan lokuta; Jan kati ya kamata a ba ni..
“Hankalina ne ya gushe a lokacin da bai dace ba, kuma ba ni wa wani kwakkwaran uzuzi. Me ya sa ba za a busa an yi keta ba? Ya hakan za ta yiwu?”
Klopp ya fusata matuka saboda rafalin ya ki bai wa Liverpool bugun tazarara bayan kan ketar da Bernado Silva na City ya yi ywa dan wasan gaban Liverpool, Mohamed Salah.
A kan haka ne ya nemi hucewa a kan mataimakin alkalin wasan san, nan take kuma alkalin wasan ya daga masa jan kati.
Har yanzu dai ba a bayyana hakikanin kalaman da Klopp ya furta da suka sa alkalin wasan yanke masa hukunci da jan kati ba.