A ci gaba da shari’ar Frank Geng Quanrong, dan Chinan nan da ake zargi da kisan budurwarsa, Ummu Kulsum Sani Buhari (Ummita) a Jihar Kano, a ranar Alhamis an kai ruwa rana tsakanin lauyoyi.
A zaman kotun dai na ranar Laraba, dan China ya amsa cewa shi ne ya kashe Ummita ta hanyar caccaka mata wuka.
Amma a zaman kotun na ranar Alhamis, lauyar gwamnatin Kano, Barista A’isha Mahmud da kuma lauyan wanda ake zargi Barista Muhammad Balarabe Dan- Azumi, sun fafata sosai.
Idan ba a manta ba, a zaman kotun da ya gabata, lauyan dan Chainan, Barista Muhammad Balarabe Dan-Azumi ya yi alkawarin gabatar da wata yarinya ’yar kasar Sin da take aiki a gidan Frank Geng a matsayin shaidarsa ta karshe.
Ana dai tuhumar Geng Quarong da laifin hallaka tsohuwar budurwarsa Ummita.
To sai dai lauyan Geng Frank, ya gabatar da wani kwararren likitan mafitsara, Dokta Abdullahi Abubakar daga Asibitin Mafitsara na Abubakar Imam da ke Kano, maimakon shaidarsa da ya bayyana wa kotun zai gabatar .
Daga nan ne lauyar Gwamnatin Kano ta yi suka kan shaidar, wadda ta roki kotun ta sa lauyan wanda ake tuhuma ya ba su ragowar shaidun da zai gabatar a rubuce.
Alkalin Babbar Kotun Jihar Kano wacce ita ce ke sauraron karar, Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ya karbi rokon lauyar ta gwamnatin Kano.
Lauyar gwamnatin ta kara da cewa sai sun yi nazarin abubuwan da likitan ya fada domin su gano kwarewarsa da kuma ingancin takardunsa na karatu da ya bayyana a gaban kotu.
Lauyan ya bayyana cewa sun gabatar da likitan ne saboda yadda Frank Geng ya shida wa kotun cewa marigayiyar ta rike masa makarfafa a lokacin da suke kokawa a gidansu da ke Janbulo Kano.
Cikin tambayoyin da likitan ya amsa har da wasu dalilan da kan sa mutum ya ceci kansa bayan an rike masa makarfafa inda ya bayyana cewa daga ciki akwai jin tsoro da kokawa da kuma kare kai daga abin cutarwa.
Alkalin Kotun ya dage ci gaba da sauraran shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu, 2023.