✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan masu zanga-zanga: A hukunta jami’an tsaro —HURIWA

Ƙungiyar ta buƙaci Tinubu ya bincika kisan masu zanga-zangar tsadar rayuwa da ake zargin jami'an tsaro ya

Ƙungiyar Marubutan Kare Haƙƙin Ɗan Adam (HURIWA) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da na jihohi su gudanar da bincike kan kisa ’yan Najeriya a lokacin zanga-zangar yunwa a kasar.

Shuagaban ƙungiyar, Kwamred Emmanuel Onwubiko, ya buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yabkafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin bincikar lamarin.

Ya bayyana cewa, “Bisa la’akari da rahotannin manyan kafofin watsa labarai da ke nuna yadda zanga-zangar yawan ta rikiɗe zuwa tashin hankali da kisan mutane 22 a yankin Arewa — duk da cewa a Kudu ba a samu tashin hankali sosai ba.

“HURIWA a’na kira da a gudanar da bincike a gano jami’an tsaron da ke da hannu a kashe-kashen a kuma hukunta su daidai da doka.

“Ƙungiyar tana gargaɗi cewa rashin rashin humubta masu laifi ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba,” in ji Onwubiko.

Ya ci gaba da cewa, “rashin hukunta masu laifi na iya haifar da makamanciyar zanga-zangar #ENDSARS.”

Ya kuma bukaci kwamitin ya kasance ƙarƙashin jagorancin tsohon alƙalin Kotun Ƙoli da wasu mutane biyar daga ba ɓangarori daban-daban masu zaman kansu da na gwamnati domin sakamakon binciken ya samu karɓuwa.

A cewarsa, aikin kwamitin ya kamata ya ƙunshi binciko rawar da jami’an tsaro suka taka wajen rasuwar masu zanga-zangar.

Kazalika Onwubiko ya kuma buƙaci gwamnatocin jihohin da aka samu tashin hankali — Kano, Neja, Yobe da Kaduna — su binciki kisan da ake zargin jami’an tsaro da aikatawa, sannana su haɗa kai da kwamitin bincike na ƙasa domin yanke hukunci.

Suma a haka ya yi tir da yadda bata-gari suka yi amfani da zanga-zangar waje fasa shaguna da sace-sace.