Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta biya diyyar Dala 750,000, ko kuma CFA miliyan 435, ga iyalan tsohon shugaban kasar na mulkin soji, Janar Ibrahim Bare Mainassara, wanda sojojin kasar suka yi wa kisan gilla a 1999.
A zaman kotun na ranar Juma’a a Abuja, ta bayyana cewa magadan da za a biya diyyar sun hada da matar marigayi Janar Bare Mainassara da ’ya’yansa biyar da ’yan uwansa mutum 11.
- Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Nijar ta biya iyalan Bare Mainasara
- Idan na samu aikin gadi zan bar kasuwanci — Matashi
Alkalan sun yi ittifaki cewa “An take hakkin Shugaba Ibrahim Bare Mainassara na ci gaba da rayuwa”, suka kuma yi tir da kisan gillar da aka yi mishi.
Takardar hukuncin kotun ta tsara cewa daga cikin CFA miliyan 435 na kudin diyyar ran Janar Bare Mainassara, za a ba wa matarsa CFA miliyan 75; ’ya’yansa biyar kuma kowannensu za a ba shi CFA miliyan 50; sannan ’yan uwansa su 11 kuma kowanne za a ba shi CAF miliyan 10.
Kotun mai alkalai biyar a kan shari’ar ta yanke hukuncin biyan diyyar ce bayan karar da mutum 11 daga cikin iyalan mamacin suka shigar a shekarar 2013, suna neman ta tilasta wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta gano wadanda suka kashe shi, domin su fuskanci hukunci.
A ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 1999 ne sojoji masu juyin mulki suka bude wa Janar Ibrahim Bare Mainssara wuta suka kashe shi nan take a filin jirgin sama, shekara uku bayan ya karbe mulkin kasar a sakamakon wani rikicin siyasa.
Janar Mainassara, ya mulki kasar Jamhuriyar Nijar ne daga shekarar 1996 zuwa lokacin da aka kifar da gwamantinsa a juyin mulkin da aka kashe shi a shekarar 1999.