Yayin da wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano a ranar Litinin ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW), malamai, masana da sauran jama’a na ci gaba da tofa albarkacinsu.
Kotun da ke zaman a unguwar Hausawa ta yanke wa Yahaya Sharif hukuncin ne bayan da ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, wanda alkalin kotun, Khadi Muhammad Ali Kani ya ce ya saba wa sashe na 382, karamin sashe na shida na kundin shari’ar Musulunci na jihar Kano na shekara 2000.
Matashin dai ya tura wani sakon murya ne ta dandalin sada zumunta na WhatsAp inda ya yi batanci ga Ma’aiki a watan Fabrairu, wanda hakan ya jawo zanga-zanga neman a hukunta shi.
Yawancin wadanda suka yi tsokaci sun bayyana gamsuwa da hukuncin kotun, da cewa hakan zai kare afkuwar tarzoma ko kuma mutane su dauki doka a hannunsu.
‘Hukuncin ya yi daidai’
Sanannen malamin Musuluncin nan a Kano, Shaik Aminu Ibrahjim Daurawa ya ce hukuncin zai kwantar da hankali a jihar.
Daurawa wanda tsohon shugaban hukumar Hizbah ne ta jihar ya kara da cewa dole a kiyaye addini, rayuka, dukiyoyi, hankali da kuma nasabar mutane matukar ana son zaman lafiya a al’umma.
Ya ce, “Idan gwamnati za ta rika hukunta dukkan wani mai hankali da ya aikata irin wannan laifin kuma kotu ta tabbatar masa da laifinsa, to tabbas za a samu zaman lafiya a kasa.
“Amma idan hukuma ta kyale irin wadannan mutanen suka ci gaba da yawo ba tare da hukunci ba, za a iya samun barkewar tarzoma saboda mutane na iya daukar doka a hannunsu.
“Muddin ana hukunta masu irin wadannan laifukan, musamman wadanda suka shafi addini za a samu raguwar aikata su.
“Hukuncin zai dawo da kwarin gwiwar da mutane ke da shi ga bangaren Shari’ar Musulunci kuma zai zama izina ga masu kokarin yin batanci ga abun da sama da mutum biliyan daya da miliyar 500 suka yi imani da shi a fadin duniya.
“Kazalika, hukuncin zai taimaka wa iyaye wajen tarbiyyar ’ya’yansu su san muhimmancin addini; ko nasu ko kuma na wadansu”, inji Shaikh Daurawa.
‘Haka Musulunci ya tanada’
Shi ma da ya ke nasa tsokacin, wani babban malami a Kano kuma jigo a Darikar Tijjaniyya, Shaikh Muhammad Nur Arzai ya ce hukuncin kotun ya yi daidai da tanade-tanaden Musulunci kan batanci.
“Matukar aka gurfanar da wanda ake zargi da laifin gaban kuliya kuma aka same shi da laifin, hukuncinsa shi ne kisa, amma hukuma ce za ta kashe shi ba wai mutane ba.
“Laifin da ya shafi batanci ga Allah ko manzonsa (SAW), ko da wanda ya yi ya tuba daga baya ba za a karbi tubarsa ba, sai an tsayar masa da haddi.
“Saboda haka babu wanda zai aikata wannan laifin a kuma kyale shi haka”, inji Shaik Arzai.
— Izina ce ga wasu
Wani mazaunin Kano, Ahmadu Mustapha ya ce duk da yake hukuncin ya zo musu da ba-zata, amma shi ne abun da ya dace.
“Ya aikata ba daidai ba kuma doka ta yi halinta a kansa, ka ga akalla zai zama izina ga wasu.
“Ya kamata a kawo karshen wannan abun gaskiya. Mutane ya kamata su san mutuncin Ma’aiki (SAW), duk wanda ya yi batanci gare shi ya kamata a hukunta shi”, inji Ahmadu.
Shi kuwa Shugaban kungiyar Muryar Talaka, Balarabe Yusif Babale Gajida cewa ya yi, “Dalilin da ya sa a baya mutane ke daukar doka a hannunsu shi ne ganin masu aikata irin wannan laifin suna yawo ba tare da an hukunta su ba. Ina fatan gwamnati za ta zartar masa da hukuncin”.
— Kungiyoyin kare hakkin dan Adam
A bangare daya kuma kungiyoyi kare hakkin bil’Adama sun ce hukuncin ya yi daidai tunda haka Shari’ar Musulunci ta tanada.
Shugaban kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Global Community for Human Rights Network da ke Kano, Karibu Yahaya Lawan Kabara ya ce sashe na 392 na Kundin Shari’ar Jihar Kano ya tanadi hukuncin daurin shekaru biyu idan laifin an yi shi ne kan wanda yake da tarin magoya baya.
Sai dai ya ce idan laifin ya shafi Allah, Ma’aiki (SAW) ko sahabbansa, hukuncin kisa ne dokar ta tanada.
Idris Ibrahim, wanda ya jagoranci wasu gungun matasa da suka yi zanga-zangar ganin an hukunta Yahaya a watannin baya ya bayyana farin cikinsa da hukuncin, yana mai cewa ranar da suka dade suna jira ke nan.
Ya kuma yaba wa hukumar Hizba ta jihar saboda jajircewarta wajen ganin an hukunta mai laifin.
“A dan tsakannin nan an samu akalla mutum hudu zuwa biyar suka aikata irin haka wanda ya jefa damuwa a zukatan mutane da dama kasancewar ba a hukunta ko daya daga cikinsu ba, amma yanzu Alhamdulillah da kotu ta fara yanke hukuncin, mutane za su samu natsuwa.
“Duk da dai mun ji an ce wai yana da damar daukaka kara, amma muna addu’a kada Allah Ya ba shi ikon yi, in kuma ya yi kada Allah Ya ba shi nasara”, inji Idris.