✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiraye-kirayen kiwon karsanar kambama karkara (1)

Kwance-tushe Kwasar taushe Kwas-kwas din kushe-kushe Kwalkwalin karime-karimen kwabon tashe Kutungwilar wawushe-wawushe   An dai haifar da matsala Na karkara na shan bulala Jinane sun…

Kwance-tushe

Kwasar taushe

Kwas-kwas din kushe-kushe

Kwalkwalin karime-karimen kwabon tashe

Kutungwilar wawushe-wawushe

 

An dai haifar da matsala

Na karkara na shan bulala

Jinane sun malala

Miyagu na ta kisan gilla

An dai karke da lalala

 

Magabta sun kwashi salala

Gari da dawa ana ta tsilla-tsilla

Gararumar dukiyar sata zalla

An haifar wa al’umma kwararar kwalla

Lallai mui karatu dalla-dalla

 

Rubdugun ragargazar ruga

Raga-ragar ragga

Rakin rashin riga

Rububin ragon raga

Ruge-rugen rikon rogo raga-raga

 

Kwanaren karo-karo

Sasarin sunkurun soro

Tumurmutsin tumbatsar taro

Kwane-kwanen kwararo-kwararo

Jimirin jinkirin Jauro

 

Makekiyayar makiyaya

Matattara mikakkiya

Mamayar makiyaya

Makokin marainiya

Matakin makauniya

 

Fifi-dallo

Futa-toro da Futa-djallo

Fulfulden fafutikar Fullo

Naman bisashe kilo-kilo

Agwagi da talo-talo

 

Ko dai a daina cin nama

Tabahuwa na sa hamma

Makiyaya a kara himma

Dabarar zamani ce makama

Gararambar daji ta rasa kima

 

Karamar hukuma

Kui masana’antar jima

Karofin rini ma a tama

Kowa ya zo a kama

Arziki ya kankama

 

Yau gari ya washe

An zo ana ashe- ashe

Kwakware an yashe

Dauke-dauken  daddakowar tushe

Komai-da-komai an kwashe

 

Bambamin Bahaushe

Bagun burgar Baushe

Bushe-bushen Barbushe

Bini-binin bin bisashe

Basarwar batun Bajamushe

 

Mu dai kauce wa cin mushe

Cinikinmu ya zam da kowane sashe

Kafar cutar miyagu a toshe

Kullin makirai ya rushe

A kwashi tuwo da miyar taushe

 

Hadin gwiwar haure-haure

Harbin hare-hare

Hargowar Harare-harare

Harigidon hure-hure

Hankoron hambare-hambare

 

Sasarin shure-shure

Artabun ature

Aringizo a tare

An yi taga-taga an tattare

Dumuiniyar danne dukiya a daure

 

An haka kwakware

Ana ta kwanare

Sana’ar na-duke da tsumbure

Kora bisashe ana are-are

Kai gwanayen kakarar kakare

 

’Yar karamar hukuma

An maisheta guzuma

An kwashe gararuma

Mahukuntan jiha na ta fama

Sun danne fama-famai da dama

 

Ba mai taimakon talakawa

Ci-amanar camama ba ta cewa

Kawuntsila na gudawa

Gwamna gwarangwam gangankon gamawa

Shi da mukarrabansa ke ganawa

 

Kitimurmurar karmamin kara

Labi-labi ake bi na kunya

Lawali ma ba wata hanya

An kwashe matsabbai ana dirkaniya

Gamin-gambizar hakkoki an tara

 

Fantamawar fatara

Baranbarama karara

Asusun asassa asara

Dibar kudin nan kwara

Wasu sun kwashi gara

 

Kauyukan kayau

Biranaen Barau

Na alatu da kayan karau

Ana tauna gyada marau-marau

Talakawa ba sa gani garau-garau

 

Kwashe-kwashen Kwasau

Jimamin Jimrau

Birgimar Barau

Karajin kasurar Kosau

Tone-tonen tunanin Tunau

 

Make-maken Makau

 

Murtukewar Mantau

Kauyukan fankan fayau

Birin Dikko a kai Kumayau

Gwamna Mai-samari na birnin Korau

 

Gunjin Gwamna el-Rusau

Ja-gaban jan talaka talau

Ciki da baka lafiya lau

Gari yai sumul kalau

An fara gani ko ba tabarau

 

Kakarin kassara karkara

Kurarin kaza kyarkyara

Gungurawar kunkuru gangara

Gararumar garabasar gara

Gogoriyon gudun gyara

 

Babban bakin Ce-ce-ku-ce

Yai takaddamar zance

Akai ta ka-ce-na-ce

Wai karamar hukuma ce

A jimurdar hadakar jiha ce

 

Masu fashin baki

Sun niki gari niki-niki

Sun bijiro da bukatar kawar da tarnaki

A daina kwasar kudi ai surkuki

An gaza farde gayaunar karkara da taki

 

An ce an jinka musu kudi

Masu mulki  na kwankwadar modar modi

Talaka na fama da zogi da radadi

A kasa ana ta rawar dodon kodi

Kar a koma gidan jiya baibaye da rudi

 

A zo ai makaranta

Rubuta ka karanta

Farfajiyar Bokan Turai ta wadata

Moriyar rayuwa a fasalta

Ai taro na mahankalta

 

Ai aiki tukuru a samu yalwa

Mutan karkara su ce yawwa

Shukar masara da dawa

Ganyayyakin  rama da yakuwa

Tuni sai a daina kuwwa

 

Zamanmu yai ban shawa

Mu caba ado da kawa

A zo ana kyakkyawa

Musafiha ta zam tafawa

Bunkasarmu ta zarta gudun laulawa

 

Ina kike ne Tabawa

Har da Malama Hauwa

Wata ma lakabinta Yalwa

Ku dai dora mana sanwa

Karin kumallonmu ya zam sabkewa

 

Sai a lalubo sana’a

Ko an samu sa’a

Don a daina yi mana ba’a

Karatunmu mai manhajar kira’a

Juhala mu ce a’a

 

Mu dai mu zam masu da’a

Tarairayar biyayya kyautata dabi’a

Alwala ta zam ba lam’a

Mu zam masu kana’a

Kyautata mu’amalar jama’a

 

Hadarin kasa maganin mai kabido

A dai yi kyakkyawan kirdado

Batun ingarma bai bukatar ado

Ku dai firfito dododo-dododo

Kar ku bari ai muku dodorido

 

Karsanar kiwon karkara

Karmamin kara

Kurarin kakara

Karambanin kan-kara

Kakarin kukan kura

 

An haifar da asara

Yanzu ake son a gyara

Wasu sun buge da wasan dara

Wasu na ta tataburzar tabara

Ai mai yiwuwa kowa ya sarara

 

A shawo kan rigingimu

Matsiyatan miyagu su zam kamammu

Mu yasar da dimuwar dimammu

Masu kitsa fitinu a cafke su dumu-dumu

Sungume da bisashe manya da ramammu

 

Mahukunta ai abin da ya dace

Diyyar karsanar da aka sace

Bujimin da ya bace

Garken garakan da ya balbalce

Sai a daina ce-ce-ku-ce

 

Tuni aka fasko masu kwace

Haushin fushinsu ya za a huce

Tarkon cutarsu ma a kubce

Ka da mugun aikinsu ma ya zarce

 

A zo ana bilinbituwa a karkace.

 

 

 

Ina dokar kunshe tushe

 

Kara zube ake rashe-rashe

 

Wani yai kwararar ruwan zafi tafasasshe

 

An gaza kawar da illar ta gushe

 

Yaushe za a fanshe

 

 

 

Ai aiki kodayaushe

Ka da ai dawurwurin yaushe-yaushe

Ko a zo ana ta soshe-soshe

Barna tai ta bashe-bashe

Wurgin wukaken washe-washe

 

Karshen tatsuniya kurungus

Mun gaji da kus-kus

Almara ce tattare da algus

Da musun mus-mus

Karashen karkarewa kiris

 

Kauyuka na cikin takura

Birane ana ta bulkara

Mahukunta ka da a makara

Talaka na shan makara

Tsintsiya a kyautata shara

 

Ai aiki ba jira

A nemi hanyar tsira

A daina tufka da warwara

A kange kowa daga asara

Sai manufa tagari ta shahara

 

Karamar Hukuma

Mahukunta ai ta fama

Wajen hana hadakar handama

Haramben Hauro daga sama

Dumuiniyar danniya ta shige duma

 

A dai bi doka

A rage yawan duka

Al’umma na ta kuka

Al’amuran aika-aika na shan suka

A kyautata kiwo damina da kaka