Masana sharia’a sun bayyana cewa, zalunci ne rashin fallasa sunayen mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci.
Sun bayyan cewa rashin fallasa wadana ake tuhumar zai haifar da zargi, hasali ma in dole a fadi sunayensu, inda dai ba kudundune za a yi shari’ar ba.
- Yara 775,000 sun daina zuwa makaranta a Katsina saboda rashin tsaro
- Ziyartar Tinubu: Yadda su Wammako suka kashe N265m
A kwanakin baya ne Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana wa Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo na 76 a birnin New York na Amurka cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta fallasa sunayen mutanen da ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci da kudade ba.
Kakakinsa Umar Jibrilu Gwandu ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar inda ya ce, batun bayyana suna ko kunyata masu laifi yana da ka’ida a kundin tsarin mulki, domin yana farawa ne da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu, sannan ya kare idan an samu mutum da laifi.
Ya ce Ofishin Binciken Laifuffuka na Kasa ya binciki kundaye sama da 1,000 na tuhume-tuhume da ake yi wa masu daukar nauyin ta’addanci na Kungiyar Boko Haram, wadanda daga cikinsu aka gurfanar da 285 a gaban kotu.
Sai dai wannan matsayi ya jawo suka daga masana da ’yan adawa da shugabannin addini, cikinsu har da Bishop din Cocin Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, wanda ya zargi gwamnatin Shugaba Buhari da rashin nuna gaskiya wajen yaki da ’yan ta’adda da suke kashe mutanen kasar nan.
Ya nuna shakku kan abin da ya sa gwamnati ta ki fitowa da sunayen mutanen da ake zargi da daukar nauyin ayyukan ta’addancin Boko Haram.
Aminiya ta tattauna da masana shari’a game da matakin kin bayyana sunayen wadanda ake zargi da daukar nauyin ta’addanci da masu aikatawa.
Kin fallasa masu daukar nauyin ’yan ta’adda zai haifar da zargi – Barista Abba Hikima
Barista Abba Hikima Fagge ya ce kin bayyana sunayen da gwamnati ta yi ba laifi ne a cikin doka ba, sai dai hakan zai iya haifar da zargi a wurin jama’a.
“Ya kamata mutane su sani cewa rashin bayyana sunayen mutanen da gwamnatin take zargi da tallafa wa Boko Haram ba laifi ta yi ba.
“Saboda ba nauyi ne (duty) a kanta ta sanar ba. Abu ne na ra’ayin kanta idan ta so ta sanar, idan kuma ta so ta bari,” inji shi.
Sai dai Barista Fagge ya ce tunda gwamnatin ce da kanta ta dauki alkawarin bayyana sunayen, to, ya kamata ta cika alkawarin don ta toshe barakar da kin yin hakan zai haifar.
Ya ce, “Gwamnati da kanta ta dauki alkawarin cewa za ta sanar ko kuma za ta bayyana sunayen mutanen da take zargi da wannan aiki, to, ya kamata ta cika wannan alkawari, kin yin haka zai haifar da abubuwa biyu.
“Na farko za a rika kallon gwamantin a matsayin wacce ba ta san abin da take yi ba. Na biyu yin hakan zai iya sanya zargi a zukatan jama’a.
“Dole ne mutane su fara zargin cewa watakila da sa hannun gwamnati ko kuma wadansu na kusa da ita a cikin lamarin, don haka ta ki fitowa fili ta bayyana sunayen mutanen da sauransu.”
Rashin bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci zalunci ne – I. G. Maryam
Wani dan gwagwarmaya Malam Ibrahim Garba Maryam wanda shi ne Shugaban Kungiyar Samar da Daidaito a Al’amuran Gwamnati da Al’umma, ya ce kin bayyana sunayen mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta’addaci a kasar nan da gwamnati ta yi da cewa zalunci ne.
Ya ce, “Mutane sun yi ta addu’ar Allah Ya tona asirin wadanda suke da hannu a cikin wannan lamari. Yanzu sai ga shi an ce ana zargin wadansu mutane sama da 400 da daukar nauyin wannan harka ta ta’addanci.
“Ashe kin bayyana sunayen wadanan mutane tare da yi musu hukunci ya zama an zalunci al’umma.”
Haka I. G. Maryam ya ce idan gwamnati ta ci gaba da kin bayyana sunayen mutanen da ake zargi, to, za ta zama abar zargi cewa da hannunta a ciki ko kuma da hannun wadansu na kusa da ita.
Ya ce, “Idan za mu iya tunawa lokacin gwamnatin baya an zargi Shugaban Kasa Jonathan da hannu a harkar Boko Haram, a wancan lokaci ma cewa aka yi shi ne shugaban ’yan Boko Haram.
“To yanzu kuma da wannan gwamnati ta zo ta masu gaskiya da adalci wadanda suka ce za su gama da Boko Haram a wata uku, sai ga shi harkar ta’addacin ta ci gaba.
“To abin tambaya shi ne a yanzu kuma wane ne yake yi. Amsar daya ce ke nan ya zama wadannan shugabannin su ma su ne suke gudanar da ta’addancin.
“Idan kuma ba su ba ne to na kusa da su ne wadanda ba za a iya hukunta su ba.
“Da ma ana zargin cewa duk wanda ya shiga Jam’iyyar APC an yafe masa laifuffukansa.
“To muna zargin wadancan mutanen da aka ki bayyana sunayensu ’yan APC ne wadanda kuma za a yafe musu laifin da suka aikata na kashe-kashen rayukan jama’a da barnatar da dukiyar al’umma da ta kasa da tayar da hankalin jama’a a sassan kasar nan.”
Malam I.G. Maryam ya ce, “Idan aka duba duk inda ake yaki idan babu masu daukar nauyi, dole yakin ya zo karshe.
“Amma idan ba a bankado masu daukar nauyin yakin ba, to, fa babu ranar da yakin nan zai zo karshe.
“Don haka idan gwamnati ba ta bayyana wadannan mutane da ake zargi tare da hukunta su ba, to, ta sani yakin sai abin da Allah Ya yi.
“Irin wannan sakaci da gwamnati take yi shi ya janyo tun ana yakin a iya bangaren Arewa maso Gabas, har ya watsu wasu bangarorin kasar nan.
“Kuma idan har ba a yi da gaske ba, to, abin Allah kiyaye, Allah ne kadai Ya san iya inda abin zai tsaya.”
Idan ba a kudundune za yi shari’ar ba dole a bayyana sunayensu – Barista Mainasara
Shi kuwa masanin shari’a da difilomasiyyar duniya, Barista Mainasara Ibrahim Kogo, ya bayyana rashin gamsuwa kan hanzari da Gwamnatin Tarayya ta gabatar na rashin dacewar bayyana sunayen wadanda ake zargi da tallafa wa ’yan ta’addan.
Barista Mainasara wanda ya bayyana haka a yayin amsa tambayar Aminiya kan jawabin Ministan Shari’a, Abubakar Malami, cewa ba za a bayyana sunayen wadanda ake zargin ba sai kotu ta tabbatar da hakan.
Ya ce bayanin Ministan ya dogara ne da Sashi na 36 sakin layi na 5 na Kundin Dokokin Najeriya da ya yi bayanin cewa, “Komai girman laifin da ake ji ko ganin wani ya aikata, wanda ake zargin yana matsayin marar laifi ne har sai kotu ta same shi da aikata hakan tukuna.
“Ma’ana ba a cewa wane ko wance ta aikata laifi kaza, har sai an gabatar da kwararan hujjoji da suka tabbatar da aikata hakan, sannan a karshe kotun ta gamsu cewa mtumin ya aikata laifin da ake zargin sa da aiaktawa.”
Lauyan ya ce wani dalili da watakila gwamnatin take gudu shi ne, daukar doka a hannu da jama’a suke yi inda ake auka wa dukiya ko kadarori da ka iya kaiwa ga asarar rai da sunan zanga-zanga.
Ya ce akwai kuma matsalar tsangwama a kan wanda ake zargin ko iyalansa tun kafin kotu ta same shi da laifin da ake zarginsa da aikatawa.
Sai dai ya ce Sashi na 230 zuwa na 304 na Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa kotu cikakken iko da hurumin yanke hukunci a kan duk wani laifi da aka aikata, kamar na cin hanci da rashawa ko wanda ya shafi bangaren tsaro kamar ta’addanci.
“To idan Babban Lauyan Tarayya ya ce ba za a bayyana sunayensu ba ban ga ta yadda za a yi shari’ar ba, saboda idan aka zo gabatar da shari’ar, dole ne a bayyana sunayen wadanda ake yi wa shari’ar, idan dai ba a kudundune za yi shari’ar ba,” inji masanin shari’ar.
Barista Kogo ya ce saboda haka, in dai ba a asirce za a yi shari’a ga wadanda ake zargi ba, to, ba makawa ko ana so ko ba a so, dole ne a bayyana sunayen wadanda ake zargin.
Ya ce, a karshe wadanda ake tuhumar za su tabbata wadanda ba su da laifi, idan kotu ba ta same su da aikata abin da ake tuhumarsu ba.
Idan kuwa kotu ta same su da laifi, sai a tasa keyarsu zuwa gidan kaso ko a kwace kadarorinsu, ko a sare musu kai, ya danganci girman laifin da kuma hukunci da kotun ta yanke.
Barista Mainasara ya ce ba daidai ba ne gwamnati ta jinkirta lamarin, inda ya bukaci a gaggauta gabatar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu ko don yadda hankalin jama’a ya raja’a a kai.
“Wannan yana daya daga cikin dalilan da muka jima muna neman a kafa kotuna uku na musamman da suka hada da ta yaki da cin hanci da rashawa ciki har da damfara ta Intanet da ta aikata ta’addanci da kuma ta shari’ar zabe.
“Dole ne gwamnati ta yi haka idan da gaske take yi tana son ta tsaftace lamarin ta hanyar magance tsaikon da ake fuskanta.
“Idan ma ba za a kafa kotunan ba, to a hanzarta gabatar da su a gaban kotunan da ake da su,” inji shi.
Ya ce ba daidai ba ne a rika daukar wadansu a matsayin shafaffu da mai, alhali idan talaka ya aikata laifi ba a sassauta masa wajen hanzarta gurfanar da shi a gaban shari’a.
Shi ma wani dan fafutikar kare hakkin jama’a da Aminiya ta zanta da shi mai suna Malam Khalid Isma’il, ya ce jawabin na Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya yi hannun riga da ikirarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake yi a kullum cewa zai yaki matsalar cin hanci da kuma matsalar tsaro.
“Saboda ai ba lokacin da kasar nan ta fi bukatar bincike da kuma gurfanar da wadanda ake tuhuma irin wannan lokaci, bisa la’akari da yadda gwamnati take ikirarin ta kashe makudan kudi a harkar tsaro da kuma bashin da take ciyowa, amma ba tare da an ga tasirin abin ba,” inji shi.