A kwanakin baya ne aka yi wa wani dan kasar Thailand tiyatar gaggawa domin cire masa wani kifi da ya shige cikin makogwaronsa.
An ce kifin ya yi tsalle ne daga cikin ruwa ya wuce cikin bakinsa lokacin da bakin ke bude kuma kafin kifin ya bude kayoyinsa a makogoron mutumin.
- Wahalar fetur ta sa an mayar da hutun mako kwana 3 a Sri Lanka
- Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya mutu bayan ya taka nakiya a Mali
A cewar kafofin labarai na Thailand, mutumin da kifin ya shige masa makogwaron mai sana’ar kamun kifi ne.
An bayyana cewa, mutumin da aka sakaya sunansa, yana tsakiyar kamun kifi ne a cikin wani kogi, kuma a daidai lokacin da ya taso ya sha iska, sai wani kifi jinsin karfasa (Anabas) ya yi tsalle daga cikin ruwan ya wuce kai-tsaye zuwa cikin bakinsa.
Da mutumin ya yi kokarin yin numfashi sai kifin ya shige cikin makogwaronsa inda ya makale.
An bayar da rahoton cewa, hadarin ya auku ne a ranar 22 ga Mayun bana a Lardin Phatthalung na kasar Thailand, kuma mutumin ya yi kusan rasa ransa.
karamin kifin ya sa masuncin yin numfashi da kyar, amma ya yi sa’a an gano shi a manne a cikin makoro, bayan wadansu sun ga masuncin a cikin mawuyacin hali inda suka kai shi asibitin Lardin Phatthalung.
Ayarin likitocin sun yi nasarar ceto rayuwar mutumin ta hanyar ciro kifin wanda jini ya lullube shi a lokacin da suka yi aikin tiyata na tsawon sa’a daya.
Tun daga nan ya samu lafiya kuma a karshe aka sallame shi daga asibitin.
“Damar faruwar hakan kadan ce. Ban taba ganin irin wannan tsautsayin ba,” kamar yadda Dokta Sermsri Pathompanichrat ya shaida wa manema labarai.
Ya kara da cewa, “Likitocinmu sun yi aiki tukuru don rage raunin da masuncin zai iya samu lokacin aikin. Sun yi nasarar ceto ran masuncin.”
Samun kifi mai rai a cikin makogwaron mutum ka iya zama abin fargaba saboda motsin da zai rika yi da suka da kaya a cikin makogoron.