An gano gawar wani masunci da ya ɓace a cikin wani kada a Arewa maso Gabashin Ostireliya, in ji Hukumar ’Yan sandan kasar.
Masuncin da aka sakaya sunansa mai shekara 40 ya ɓace ne bayan farmaki da ake zargin na kada ne a kusa da gadar Kogin Annan da ke Arewa Mai Nisa ta yankin Queensland a yammacin wata Asabar.
Wata sanarwa da ’yan sandan Queensland suka fitar ta ce “Ana gudanar da aikin tantancewa a hukumance, amma an yi imani cewa gawar ta wani ɗan Jihar New South Wales mai shekara 40 da ya ɓace.”
“Za a gudanar da karin gwaji don gano hakikan asalin wanda ake nema.”
’Yan sandan sun ce an dakatar da aikin neman mutumin da ya ɓace .
Tun farko, a ranar Litinin, kafofin watsa labarai na kasar sun ruwaito mai magana da yawun Ma’aikatar Muhalli, Kimiyya, da Ƙirkira ta Ƙueensland yana cewa an kama wani babban kada da aka yi imani shi ne ke da alhakin farmaki da aka kai wa mutumin.
An gano kadan ne mai tsawon mita biyar, a nisan kilomita 4 daga inda mutumin ya ɓace kuma an gane shi saboda wasu alamomin hancinsa.
An ce kadan ya haura shekara goma a duniya.
Kafofin yaɗa labaran Ostireliya sun ce masucin yana cikin sana’arsa ta kamun kifi da matarsa da ’ya’yansa ne lamarin ya faru.
Hukumomin kasar sun yi bincike kan rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa an ga mutane suna ciyar da kada a kusa da inda lamarin ya faru.
Ciyar da kada ana ɗaukarsa a matsayin aikata laifi kuma ana iya hukunta wanda ya yi haka da tarar Dala 6,452 (kimanin Naira miliyan 10 da dubu 258 da 680).
Ana samun munanan farmakin kadoji biyu da matsakaita a kowace shekara a Ostireliya.
Lamari na baya-bayan nan a watan Yuli ya yi sanadin kashe wata yarinya ’yar shekara 12 a Arewacin kasar kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito.