✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida

Gidan Shark babban wurin ɗaukar hankali ne na yawon buɗe ido.

Wani kifi jinsin Shark da mamallakin Kamfanin Airbnb da ya shahara a duniya mai tsawon kafa 25 ya fusata, inda ya fito daga rufin gidan da yake saboda matakin da aka ɗauka na tilasta rufe gidan da aka ajiye shi.

Mamallakin Kamfanin wanda yake mazaunin Birtaniya ne, mai suna Dakta Magnus Hanson-Heine ya rasa wani shirin neman alfarma daga Karamar Hukumar Oxford na hana shi amfani da wurin zama na ɗan gajeren lokaci na cikin kadarorinsa da aka fi sani da Shark House (wato inda yake kiwon kifin).

Ya yi iƙirarin cewa bai samu ƙorafi ko ɗaya daga makwabtansa ba, amma kuma hukumar yankin ta gabatar masa da korafi a kan a rufe gidan AirBnbs da ke cikin birnin.

Haka kuma, a yanzu ya buƙaci baki da su zo, su ziyarci gidan yadda za su iya, inda ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da harkoki yadda zai iya.

Mutumin wanda mahaifin HansonHeine da Bill Heine, ya fara gina wannan gidan ba tare da izinin Karamar Hukumar Birnin Oxford a 1986 ba.

A shekaru biyar da suka gabata, ya bayar da hayar kadarorin a karkashin Kamfanin Airbnb na dan gajeren lokaci – amma ya sami sanarwa daga karamar hukumar a kan rufe gidan, bayan wani makwabcin yankin da ya koka game da canjin wurin zama zuwa wani wuri na ɗan gajeren lokaci.

Yanzu an sanar wa Hanson-Heine cewa, dole ne ya daina amfani da gidan na ɗan gajeren lokaci kafin 11 ga Maris, 2025 – matakin da ya yi imanin zai cutar da kamfaninsa dangane da yawon buɗe ido a Oxford gaba ɗaya.

“Gidan Shark babban wurin ɗaukar hankali ne na yawon buɗe ido, ba kawai kamar gidan iyali na yau da kullum ba ne.

“Abin farin ciki ne na sanar da jama’a domin su yi murna tare da mu, kuma zan ci gaba da yin hakan tsawon lokacin da zan iya,” in ji shi.

“Har yanzu ban ji wasu korafe-korafe daga makwabtanmu ba, ko da a lokacin da ake shirin daukaka ƙarar, kuma sufeton yankin bai samu wani nakasu ba a hukuncin da ya yanke,” in ji shi.

Ya ce ya samar da wannan wurin ne don yawon bude ido da yake daukar hankalin baki masu ziyartar wuraren da ya buɗe.

“Wasu daga cikin ’yan majalisar sun yi amfani da wannan a matsayin uzuri don samun wasu hujjoji na siyasa ta hanyar bin taswirar wani yanki na cikin gari don cin gajiyar jama’a,” in ji shi.

“Wannan bai ba da wani abu mai ma’ana ba, don taimaka wa mutanen da ke neman wuraren yawon buɗe ido.

“A bangaren yawon bude ido da masaukin baki yankin Oxford zai kasance mafi muni a gare shi.”