✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun ciro kifi mai rai daga cikin wani

Lokacin da suka bude cikin mara lafiyar, likitoci sun yi mamakin gano cewa kifi ne mai tsayin mita 30.

Likitoci a kasar Bietnam sun ceto rayuwar wani matashi ta hanyar ciro kifi mai rai, mai tsawon mita 30 daga cikinsa, inda ya ratsa a cikin hanjinsa.

A ranar 20 ga Maris aka shigar da matashin mai shekara34 a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Hai Ha da ke Lardin Kuang Ninh na Bietnam, lokacin da yake fama da ciwon ciki maitsanani.

Tunda ciwon ya yi tsanani ba a yi masa tambayoyi kan alamomin da ke damunsa ba, sai likitocin suka yi masa hoton cikin da na’urar X-ray sai na’urar ta nuna wani waje a cikinsa da hujewar hanji da wani abu a gefen tumbinsa.

Likitoci sun yanke shawarar cewa abin da ya fi dacewa shi ne yin tiyata, tare da cire abin da ake gani a cikin da kuma kokarin magance ciwon da ke jikin hanjin matashin.

Lokacin da suka bude cikin mara lafiyar, likitoci sun yi mamakin gano cewa kifi ne mai tsayin mita 30 mai rai ke rayuwa a cikin.

Bayan cire kifin, likitoci sun ci gaba da cire sashin da ya sauya launi a hanjin ta hanya mai sauki tare da kariya ga yiwuwar kamuwa da wata cuta saboda kusanci da yankin dubura.

An yi sa’a, tiyatar ta yi nasara kuma an kwantar da majinyacin.

Ya dai ba da rahoton rashin jin dadi a cikin cikinsa bayan tiyatar, kuma har yanzu yanajin ya a asibiti.

Da aka tambaye shi ta yaya kifin ya shiga cikinsa, matashin ya kasa bayar da wata cikakkiyar amsa, amma likitocin sun yi imani cewa kifin mai santsi ya taso daga dubura zuwa hanjinsa ne, ya cije shi a jikin hanjin, sannan ya shiga ciki.

Amma abin da ya firgita ma’aikatan asibitin shi ne cewa yadda kifin mai santsi ke raye a cikin mutumin.

Wannan al’amari na gano hoton kifin a cikin majiyyacin na da ban mamaki kan yadda aka yi ya shiga cikin mutumin.