An gano Hodar Iblis a cikin kifaye 13 jinsin Sharks da suke rayuwa a tekunan Brazil inda aka gwada sau 100 fiye da yadda aka ruwaito a baya da ake yi wa sauran halittun ruwa.
Masana kimiyya sun ce sun gwada kifin Sharks da suke rayuwa gabar tekun Brazil sun gano suna dauke da kwayar Hodar Iblis.
Masu bincike sun daɗe suna ba da shawarar cewa za a iya samun irin waɗannan haramtattun ƙwayoyin a cikin halittun da suke rayuwa a teku ta hanyar magungunan da masu fasakwauri ke jefawa a cikin ruwa, tare da tan-tan na Hodar Iblis da aka taɓa samu a kusa da Florida a Kudancin Amurka da Amurka ta Tsakiya.
Wani bincike da Gidauniyar Oswaldo Cruz da ke Brazil ta gudanar ya gano cewa miyagun kwayoyin da suke gurbata teku suna shafar kifin Sharks.
Masanan sun rarraba kifayen Sharks 13 na Brazil da aka sayo daga kananan jiragen ruwa na masu kamun kifi, yayin da nau’in ke shafe tsawon rayuwarsa a cikin ruwan tekun da gurbacewar yanayi ke shafa.
Daga nan ne aka gwada nama da hantar kifayen ta hanyar amfani da na’urar gwajin haramtattun kwayoyin inda aka bambanta kwayoyin halittu na cikin ruwa – don neman Hodar Iblis ta hanyar gwajin fitsarinsu kuma aka gano akwai Hodar Iblis a cikin jikinsu.
Dukkan kifayen Sharks 13 suna dauke da miyagun kwayoyin, bayan yin musu gwaji sau 100 fiye da yadda ake yi wa sauran halittun ruwa.
A farkon binciken an gano alamun kasancewar Hodar Iblis a cikin kifin Sharks, kuma an gano cewa sinadarin ya fi yawa a cikin tsokar namansu fiye da hantar.
Sakamakon binciken ya ce fannin binciken ya kasance “mai iyaka sosai” kuma ba a san illar da Hodar Iblis ɗin ke yi ga rayuwar halittun ruwa ba.
An wallafa binciken a cikin Mujallar Kimiyyar Muhalli ta Total Environment.
A watan Yunin bara, jami’an tsaron gabar tekun Amurka sun kwace fiye da kilo 14,100 na Hodar Iblis a tekun Karebiya da tekun Atlantika da aka kiyasta kudinsu ya kai Dalar Amurka miliyan 186 (kimanin Naira biliyan 301da miliyan 320).