Rundunar ’yan sandan Najeriya ta yi alƙawarin kyautar Naira miliyan 20 ga duk wanda ya kawo bayani aka kama wani ɗan kasar Birtaniya da abokinsa ɗan Najeriya da ake zargin su da neman kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu.
Rundunar ta sanar cewa tana neman mutanen biyu — Andrew Wynne (Andrew Povich ko Drew Povey) ɗan kasar Birtaniya da wani ɗan Najeriya, Lucky Ehis Obinyan — ruwa a jallo.
Sanarwar da rundunar ta fitar ranar Litinin ta ce tana neman su ne kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci, cin amanar ƙasa, laifukan intanet, da kuma haɗa baki da nufin aikata laifi.
“Duk wanda ya gan su, ya sanar da Ofishin Mataimakin Sufeto-Janar kan Binciken Ƙwaƙwaf da ke Hedikwatar rundunar a Abuja, ko ya kira waɗannan lambobi: 08035179870, 09133333785, 09133333786.
- Ƙasurgumin ɗan daban da ya addabi Kano ya mutu
- ’Yan bindiga sun kashe dan sanda da dan banga a Sakkwato
“Akwai kyautar N10,000,000 ga duk wanda ya ba da bayar da bayanin da aka kama kowane mutum ɗaya daga cikinsu,” in ji sanarwar da runduar ta fitar.
ِAminiya ta ruwaito kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, na cewa sun ƙaddamar da bincike domin gano yadda sojojin haya daga ƙasar waje suka shigo Najeriya domin kifar da gwamnatin ƙasar.
Olumuyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Litinin cewa hujjoji da kuma bayanan da suka samu daga Andrew Wynne sun tabbatar da hannunsa a yunƙurin kifar da gwamnatin Najeriya.
Ya bayyana cewa Andrew Wynne ya bayar da tallafin kuɗaɗe da kuma tsare-tsaren zanga-zangar da aka gudanar kan tsadar rayuwa da nufin amfani da ita wajen ganin an hamɓarar da gwamnaitin Najeriya.
Bugu da ƙari, dan ƙasar na Birtaniya ne ya ba da umarni tare da sanya ido kan zanga-zangar yunwar da aka gudanar a fadin kasar a watan Agusta.
Jami’in ya ce binciken rundunar ya gano cewa Andrew Wynne yana zaman haya ne a gidan Labour House da ke Abuja.
Adejobi, ya ci gaba da cewa Andrew Wynne ya kama wurin haya ne da sunan buɗe shagon sayar da litattafai mai suna ‘Iva Valley Bookshop’.
Sannan kuma shi ne ya assasa makarantar ‘STARS of Nations Schools’ domin ɓatar da sawu game da manufarsa.