An saki Beatrice Ekweremadu, Matar Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, daga gidan yari a Birtaniya bayan kammala wa’adin hukuncin shekaru shida da aka yanke mata.
An samu Beatrice da mijinta Ike da likita Obinna Obeta da laifin haɗa baki wajen amfani da wani yaro ɗan Najeriya don safarar sassan jikinsa domin ceto ’yarsu wadda ke jinya, Sophia.
- Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka
- Hisbah ta kama mutum 8 kan shirya zaɓen masu ƙwazon jima’i a Sakkwato
An ce yaron, wanda ke sana’ar talla a Jihar Legas, an yaudare shi tare da kai shi Birtaniya ba tare da sanin dalilin hakan ba.
Yayin da Ekweremadu ke ci gaba da zaman gidan yari na tsawon shekaru 10, dawowar Beatrice ta sanya mutane farin ciki a Enugu.
Jama’a da dama na addu’ar ganin an saki mijinta nan ba da jimawa ba.
Wannan shari’a na daga cikin mafi shahara da ta shafi ɗan siyasar Najeriya a ‘yan shekarun nan.