✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yara masu zanga-zangar yunwa sun sume a kotu

Yara huɗu ’yan kasa da shekaru 18 da ake zargi da cin amanar Nijeriya a lokacin zanga-zangar yunwa sun sume a kotu

Ƙananan yara huɗu sun sume a kotu a lokacin da gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da su ka zargin yunƙurin juyin mulki a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan Agusta.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da zaman nata babu shiri bayan sumewan samarin a safiyar Juma’a.

Samari ’yan ƙasa da shekaru 18 guda huɗu ne suka sume a cikin kotu a lokacin da aka gurfanar da su kan zargin su da yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.

Sumewansu sakamakon tsananin ke da wuya Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya dakatar da zaman kafin daga bisani a ci gaba da zaman bayan an fitar da su domin duba lafiyarsu.

Bidiyon yadda abin ya faru ya nuna yadda lauyoyi da ma’aikata suke ƙoƙarin taimakon yaran ’yan kasa da shekaru 18.

An kuma ga ana raba wa yaran biskit a cikin kotuna a yayin da lauyoyi ke kokawa bisa yadda aka bar wadanda ake zargin babu kula.

Samari 76 da aka tsare a jihohin Kano da Kaduna da Bauchi da sauransu ne aka gurfanar a gaban Babbar Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja kan zanga-zangar.

Ana iya tuna cewa Gwamnatin Tarayya ce ta gurfanar da waɗanda suka gudanar da zanga-zangar a watan Agusta, 2024 kan tuhumar su da laifuka 10, masu alaƙa da neman kifar da gwamnati.

Bayan karanta musu takardar tuhumar, matasan sun musanta aikata laifin.

Daga nan alƙalin ya bayar da su beli a kan Naira miliyan 10 kowannensu.

Daga nan ya ba da umarnin tsare su a Gidajen Yarin Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin.

Sharuddan sun haɗa da kawo wani babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ya mallaki lasisin tuƙi da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa ya tsaya musu.

Haka kuma za su kawo takardar kyakkyawar shaida daga iyayensu ko kamu ’yan uwansu.

Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun 2025.

Kungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Amnesty International ta bukaci a yi adalci ga yaran waɗanda suka shafe watanni uku a tsare.

Ta bayyana takaici bisa tsarewar da aka yi musu saboda sun fito bayyana ra’ayinsu da kuma ’yancinsu a cikin ƙasarsu.