Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kidayar jama’ar da aka shirya gudanarwa a 2023 za ta taimaka matuka wajen magance kalubalen tsaro a kasar.
Ya ce ana bukatar alkaluman kidayar wajen sanin hakikanin yawan mutanen kasar.
- Wadume: Kotu da daure mai garkuwa da mutane shekara bakwai
- Shin Taliban Ta Cika Alkawuranta A Afghanistan?
Buhari ya bayyana haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki kan kidayar jama’a da ta gidaje da aka yi a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Ya ce Najeriya na bukatar sabbin alkaluma wajen tsara manufofin ci gaba wadanda za su dace da muradun karni da sauran manufofin gwamnati na yaki da talauci da samar wa matasa ayyukan yi.
A cewar Shugaban, amfani da hanyoyin fasahar zamanin wajen kidayar za su taimaka ainun wajen samar da sahihan alkaluma, inda ya ce akwai yiwuwar nan da shekarar 2050 Najeriya ta zama ta uku a yawan jama’a a duniya bayan China da Indiya.
“Da hasashen da aka yi na cewa Najeriya na da mutum 216,783,381, yanzu kasarmu ce ta shida wajen yawan mutane a duniya, kuma wacce ta fi kowacce a nahiyar Afirka.
“Haka kuma, a sakamakon karuwar yawan matasa, ana hasashen Najeriya ce za ta zama kasa ta uku a yawan jama’a a duniya nan da 2050 bayan China da Indiya,” inji Buhari.