Kawo yanzu an kashe mutane 13 har lahira, an jikkata wasu 31 a zanga-zangar adawa da karin haraji a kasar Kenya.
Shugaba William Ruto ya sha alwashin daukar tsauraran mataki bayan zanga-zangar adawa da shirin gwamnatinsa na kara harajin ta rikide zuwa tarzoma da mamaye majalisar dokokin kasar.
Gwamnatin kasar ta tura sojoji domin tallafa wa ’yan sandan da suka harba barkonon tsohuwa da ruwan safi da harsasan roba domin watsa masu masu zanga-zangar.
Shugababa Ruto ya sanar a birnin Nairobi cewa “Za mu mayar da cikakken martani cikin gaggawa sanoda mutane masu hadari ne suka sace zanga-zangar.”
Ruto ya kara da cewa, “masu aikata laifukan da suka shiga rigar zanga-zangar lumana na nuwa cewa za su iya yin ta’addanci a kan jama’a da zababbun wakilansu da kuma cibiyoyin da aka kafa a karkashin tsarin mulkinmu, kuma suna sa ran za su tafi ba tare da wata matsala ba.”
- ’Yan sanda sun kashe masu zanga-zanga a Kenya
- Zargin N432bn: El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu
Masu zanga-zangar da akasarinsu matasa ne suka jagoranta sun kasance cikin lumana yayin da suke karuwa a cikin makon da ya gabata.
Amma hargitsi ya barke a birnin Nairobi ranar Talata, inda jama’a suka yi ta jifan ’yan sanda da duwatsu tare da ture shingaye suka kutsa cikin harabar majalisar dokin kasar.
A sakamakon haka aka tura sojoji don tallafa wa ’yan sandan da suka harba hayaki mai sa hawaye da ruwa da harsasan roba kan mazu zanga-zangar.
Amma wata kungiyar kare hakki na zargin cewa harsashi mai rai jami’an tsaron suka yi amfani da shi a kan masu zanga-zangar.